Sha’anin tsaro: Sojin Najeriya sun tattauna da takwararsu ta kasar Nijar

Sha’anin tsaro: Sojin Najeriya sun tattauna da takwararsu ta kasar Nijar

-Rundunar sojin Najeriya ta tattauna da takwararta dake Nijar akan matsalolin tsaro da kasashen biyu ke fama dashi.

-Kakakin jami'an sojin Najeriya Kanal Sagir Musa shine ya tabbatar mana da wannan tattaunawa wacce akayi a Dakana ta kasar Nijar

Wata gamayyar rundunar sojin Najeriya ta 8 dake Sakkwato ta ziyarci takwararta a kasar Nijar domin tattaunawa kan magance matsalolin tsaro musamman akan iyakar kasashen biyu.

A wani zancen da ya fito daga bakin kakakin rundunar sojin Najeriya, Kanal Sagir Musa, yace, “Birgediya Janar L.K.N Udeagbala shine ya jagoranci wannan tawaga zuwa kasar Nijar”. Musa ya cigaba da cewa, “tawagar ta hadu da takwararta dake Nijar a Dakana inda suka tattauna akan rashin tsaron dake addabar al’ummar jihar Sakkwato.”

Sha’anin tsaro: Sojin Najeriya sun tattauna da takwararsu ta kasar Nijar

Sha’anin tsaro: Sojin Najeriya sun tattauna da takwararsu ta kasar Nijar
Source: UGC

KU KARANTA:Yan sandan Binuwe sun kama mutum 30 cikin mako guda

A cewar kakakin, “tawagar ta kunshi jami’an hukumar yan sanda, na kwastam, na hukumar hana shige da ficen da ya saba ka’ida, hukamar DSS da sauran hukumomin tsaron gida Najeriya.”

Ya sake cewa, “a sanadiyar rashin tsaro a kan iyakar Najeriya da Nijar , an kaddamar da rundunar soji domin yin sintiri a yankin kan iyakar a watan Satumban 2018”.

Makasudin wannan tattaunawa dai shine, a duba al’amuran yan bindiga da yaduwar ta’addanci dake addabar kasashen biyu wanda ya kasance ana amfani da kan iyakar yayin aikata wadannan munanan ayyuka.

A wani labarin makamancin wannan, yan sandan jihar Binuwe sunyi babban kamu cikin mako guda inda suka samu nasarar damke mutane 30.

Bayan gudunar da bincike an saki wasu daga cikinsu wadanda aka tabbatar cewa basu da laifi su matafiyane.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Online view pixel