Tsugune bata kare ba: Gwamnatin jihar Kano za ta canjawa sarkin Kano masarauta

Tsugune bata kare ba: Gwamnatin jihar Kano za ta canjawa sarkin Kano masarauta

- Yau ne gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje za ta sauyawa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II masarauta

- Hakan ya biyo bayan kirkiro sababbin masarautu da gwamnan jihar ya yi guda hudu

- Rahotanni sun nuna cewa za a mayar da sarkin Bichi, inda za a maye gurbinsa da sarkin Bichi Aminu Ado Bayero

Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje za ta canjawa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II masarauta a yau Asabar dinnan.

A wasu rahotanni da muka samu a shafin Facebook, mun samu cewar a yau Asabar din nan gwamna Abdullahi Umar Ganduje zai canjawa Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II masarauta.

Tsugune bata kare ba: Gwamnatin jihar Kano za ta canjawa sarkin Kano masarauta

Tsugune bata kare ba: Gwamnatin jihar Kano za ta canjawa sarkin Kano masarauta
Source: Twitter

A wata hira da manema labarai suka yi da wani makusanci na gwamnatin jihar, wanda ya nemi a boye sunansa, ya shaidawa manema labarai cewa, gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Ganduje ta gama shiryawa tsaf domin maida Mai Martaba Muhammadu Sanusi II masarautar Bichi, yayin da za a maye gurbinsa da Sarkin Bichi Aminu Ado Bayero, wanda yake da ne a gurin marigayi tsohon Sarkin Kano Alhaji Dr. Ado Bayero.

Sai dai kuma da aka tambayi ra'ayoyin jama'a game da canjin masarautar da yawa sun nuna rashin goyon bayan su game da abubuwan da ke faruwa tsakanin gwamnatin jihar Kano ta Abdullahi Umar Ganduje da kuma masarautar Kano ta Mai Martaba Muhammadu Sanusi II.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta cafke wani mai amfani da sunan Manajan NNPC ya na damfarar mutane

A 'yan kwanakin nan dai ana ta samun tata burza tsakanin masarautar jihar Kano da gwamnatin jihar, bayan gwamnan jihar ya raba masarautar jihar zuwa gida biyar, domin ragewa Sarkin Kano girma a jihar.

Masarautun da gwamnan ya kara sun hada da masarautar Bichi, Rano, Karaye, da Gaya.

Sai dai kuma bayan kara masarautun gwamnatin jihar ta na ta samun kalubale daga al'ummar jihar da kungiyoyi da kuma kotu, inda al'ummar jihar suke ganin abinda gwamnan ya yi bai dace ba, sannan kuma wata kotun jihar ta nemi ta ruguje masarautun, bayan ta bayyana cewa gwamnan bai bi umarninta ba gurin kirkiro masarautun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel