Zaben 2019: Babu dalilin hana Gwamna Okorocha satifiket - CASER

Zaben 2019: Babu dalilin hana Gwamna Okorocha satifiket - CASER

Mun ji labari cewa wata kungiya mai suna “The Citizens Advocacy for Social and Economic Rights” watau CASER, ta nemi hukumar INEC ta ba Rochas Okorocha satifiket din da ke nuna cewa ya lashe zaben Sanata a APC.

Wannan kungiya ta ke cewa babu dalilin da zai sa hukumar INEC ta ki mikawa gwamna Rochas Okorocha takardar nuna samun nasara a zaben Sanata na yankin Imo ta yamma da aka gudanar a cikin farkon shekarar nan.

Babban Darektan wannan kungiya ta CASER, Frank Tietie ya bayyana cewa an keta alfarmar tsarin mulki da dokar kasa wajen hana gwamnan na APC satifiket din da ke nuna yayi nasara a zaben majalisar tarayya.

Tietie ya fadawa manema labarai cewa bai dace a hana Rochas Okorocha nasarar da ya samu a dalilin ra’ayin wani Baturen zabe ba. Tietie yake cewa doka ce ya kamata tayi aiki ba abin da Kwamishinan zabe ya fada ba.

KU KARANTA: Osun: Adeleke ya sake samun kan sa tsundum a cikin wata shari’a

Darektan yake cewa su na tunanin cewa hukumar na INEC za ta janye matakin da ta dauka na hana ‘dan takarar satifiket bayan an tabbatar da cewa shi ne yayi nasara a zaben majalisar dattawa na mazabar Imo ta yamma.

Kungiyar take cewa ba za su bari wasu tsirarru su yi wa hukumar INEC ka-ka-gida su hana ta yin abin da ya dace ba. A karshen kungiyar tace dole INEC ta tsaya da kafafunta, ba ta bari a rika juya ta saboda manufar siyasa ba.

Kawo yanzu dai hukumar zaben mai zaman kan-ta, ta gaza ba gwamna Rochas Okorocha shaidar lashe zaben da aka yi. Hakan na zuwa ne bayan Malaman zaben sun nuna cewa akwai alamar tamabaya wajen nasarar APC.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel