Hukumar EFCC ta cafke wani mai amfani da sunan Manajan NNPC ya na damfarar mutane

Hukumar EFCC ta cafke wani mai amfani da sunan Manajan NNPC ya na damfarar mutane

- Dubun wani dan damfara ta cika wanda ya kware a harkar damfarar al'uma, yayin da hukumar EFCC ta kama shi yana amfani da sunan Manajan Darakta na NNPC, Maikanti Baru ya na damfarar mutane

- An kama shi ya damfari wani dan kasar Koriya ta Kudu kudi sama da dala miliyan 4.2, da sunan cewa zai saya mishi lasisin sayen kamfanin

Hukumar yaki da ciin hanci da rashawa ta kasa ta cafke wani mutumi mai shekaru 31 a duniya mai suna Jamiu Isiaka wanda ya kware a harkar damfarar mutane, hukumar ta cafke shi da laifin amfani da sunan Manajan Darakta na Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC), Maikanti Baru, yana damfarar al'umma.

Ya kuma yi amfani da sunan mai ba wa shugaban kasa shawara ta musamman akan sadarwa, Mista Femi Adesina, wurin damfarar mutanen.

Mai magana da yawun hukumar yaki da cin hanci da rashawar, Mista Tony Orilade shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa Abuja yau Juma'a.

Hukumar EFCC ta cafke wani mai amfani da sunan Manajan NNPC ya na damfarar mutane

Hukumar EFCC ta cafke wani mai amfani da sunan Manajan NNPC ya na damfarar mutane
Source: Depositphotos

Orilade ya ce wanda ake tuhumar da wasu wasu mutane, ana zargin sun yi amfani da sunan wasu manya a kasar nan inda suka damfari wani dan kasar Koriya ta Kudu, mai suna Keun Sig Kim.

"Sun damfare shi ne bayan sun yi yarjejeniyar cewar za su sama mishi lasisin kamfanin NNPC wanda zai bashi damar sayen kamfanin.

"Mutumin ya ce ya biya sama da naira miliyan 30 a cikin asusun wanda ake zargin, a matsayin kudin samun lasisin," in ji shi.

KU KARANTA: An yankewa wani mutumi hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan an kama shi da laifin harbe saurayin 'yar shi

A cewarsa "Na tura dala miliyan4.2 zuwa bankin United Bank of Africa, mai lambar akawun 2107575870 akawun din da yake da sunan Jamiu Isiaka, abokin huldar Mista Shola Adeshina."

A lokacin da aka tsananta bincike akan Orilade ya bayyana cewa ya yi amfani da kudin wurin yin sadaka ga mutumin da suka karbi kudin a wurin shi.

A karshe hukumar ta ce za ta mika shi kotu idan suka gama binciken shi kuma suka kamo sauran abokanan huldar shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng

Online view pixel