An kama muggan kwayoyi masu dimbin yawa a Kano

An kama muggan kwayoyi masu dimbin yawa a Kano

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kama kwalayen kwayan maganin tramadol guda 303 a ranar Juma'a 17 ga watan Mayun 2019.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Mohammed Wakili ne ya tabbatar da hakan yayin taron manema labarai da ya kira inda ya ce an kama wani Chris Metuh da hannu cikin safarar miyagun kwayoyin.

Daily Trust ta ruwaito cewa an kama kwayoyin ne a wani kamfanin sarrafa kayayaki a Miller road da ke unguwar Bompai na karamar hukumar Nassarawa a garin na Kano.

An kama muggan kwayoyi masu dimbin yawa a Kano

An kama muggan kwayoyi masu dimbin yawa a Kano
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Rundunar soji ta fitar da jawabi a kan zargin yunkurin kifar da gwamnatin Buhari

CP Wakili ya ce wannan kamun babban nasara ne cikin yakin da rundunar keyi domin kawar da muggan kwayoyi da sauran kayan maye a jihar kuma ya yi kira ga jama'a su cigaba da bawa 'yan sanda hadin kai domin tsafattace garinsu.

"A cigaba da yunkurin da rundunar 'yan sanda keyi na kawar da laifuka musamman fatauci da shaye-shayen miyagun kwayoyi, rundunar 'yan sanda ta sake samun gagarumin nasara inda ta kama kwayoyi da dilalan kwayoyin.

"An kama katon 303 na muggan kwayoyi (Tramadol) a gida mai lamba 157 MIller road Bompai a karamar hukumar Nasarawa a Kano a Ugo Lab Manufacturing Company sakamakon bayanan sirri da aka samu. An kuma kama wani da ake zargi, Chris Metuh mazaunin 157 Club road," inji CP Wakili.

Kwamishinan 'yan sandan ya kuma tabbatar da kama wasu mutane hudu dauke da miyagun kwayoyi da makamai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Online view pixel