Muna aiki ta karkashin kasa don sulhunta Ganduje da Sanusi - Gwamonin Arewa

Muna aiki ta karkashin kasa don sulhunta Ganduje da Sanusi - Gwamonin Arewa

Gwamnan jihar Borno kuma tsohon shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, Kashim Shettima ya ce shi da sauran gwamnoni suna aiki ta karkashin kasa domin kawo karshen dambarwar da ke tsakanin Gwamna Abdullahi Ganduje da Sarki Muhammadu Sanusi II.

Idan ba a manta ba dai a ranar 8 ga watan Mayu ne gwamnatin Kano ta kirkiri sabbin masarautu hudu a jihar abinda wasu da yawa ke ikirarin anyi ne domin rage karfin mulkin Sarki Sanusi.

A yayin da ya ke zantawa da manema labarai a wurin taron gwamnonin arewa da aka gudanar a ranar Juma'a a Kaduna, Shettima ya ce gwamnonin ba su da ikon yin katsalandan cikin harkokin wata jiha amma dai yana sha'awar ganin an kawo karshen rashin jituwar domin cigabar al'umma.

Muna aiki ta karkashin kasa don sulhunta Ganduje da Sanusi - Gwamonin Arewa

Muna aiki ta karkashin kasa don sulhunta Ganduje da Sanusi - Gwamonin Arewa
Source: Twitter

Mr Shettima ya ce: "Gwamna Ganduje da mai martaba Sarki Sanusi sun yiwa al'ummar Borno wasu karamci da na ke alfahari da su.

DUBA WANNAN: Rikicin masarautar Kano: Bashir Tofa, Usman Bugaje da wasu manya sun saka baki

"Gwamna Ganduje ya dauki nauyin karatun marayu 200 da Boko Haram suka kashe iyuayensu tun daga frimare har zuwa jami'a.

"An samar wa yaran muhalli mai kyau, abinci kuma suna samun ilimi ingantacce a karkashin wata shirin tallafi da gwaman Kano ya amince da shi.

"A bangarensa, Sarki Sanusi ne ya sada mu da Aliko Dangote. A 2016, sarkin ya ziyarci Borno kuma bayan ya ga halin da ake ciki ya yiwa Dangote magana kuma daga lokacin Dangote ya ziyarci Borno sau uku.

"Dangote ne mutumin da yafi kowa bayar da tallafi ga wadanda rikicin Boko Haram ya shafa a Borno kuma ba zan mata cewa Sanusi ne sanadi ba. A lokacin da ya ke gwamnan CBN, Sanusi ya kafa cibiyar koyar da sana'o'i a Borno a 2013.

"Ya taimaka wurin sanar da duniya halin da muke ciki a Borno. Ba zan taba mantawa da tausayi da tallafin da Sanusi da Ganduje suka nuna wa al'ummar Borno ba haka ya sa na ke son ganin nayi sulhu tsakaninsu.

"Sai dai mu gwamnoni muna da wata ka'ida na rashin yiwa juna katsalandan sai dai muna iya yin aiki ta karkashin kasa domin ganin mun kawo sulhu.

"Ba zan iya fadawa Ganduje yadda zai tafiyar da jiharsa ba amma muna iya aiki ta karkashin kasa don yin sulhu. Da izinin Allah Ganduje da Sarki za su koma su dinke wuri guda," inji Shettima.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel