Mayakan Boko Haram sun kashe Mutane 13 a Chadi

Mayakan Boko Haram sun kashe Mutane 13 a Chadi

A yayin da ta'azzarar ta'addancin ta ya munana, kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram, ta salwantar da rayukan Mutane goma sha uku a wani kauye dake gabashin kasar Chadi kamar yadda jaridar AFP ta ruwaito.

Dakarun tsaron Najeriya

Dakarun tsaron Najeriya
Source: Facebook

Jaridar AFP ta ranar Juma'a ta ruwaito cewa, mayakan boko haram da sanyin safiyar ranar Alhamis da ta gabata sun kai hari kauyen Ceilia inda suka kashe wani basaraken gargajiya tare da iyalan sa uku gabanin kone gidan sa kurmus.

Bayan zartar da wannan mummunar ta'ada mayakan boko haram sun kashe mutane 9 a kan hanyar su ta tsarewa kamar yadda Dimouye Soiapebe ya bayar da shaida, wani jami'in hukumar tsaro a gabar tafkin Chadi.

KARANTA KUMA: Mataimakin shugaban kasa ya jagoranci karashen zaman majalisar zantarwa

A halin yanzu kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram ta salwantar da kimanin rayukan mutan 27,000 tare da salwantar muhallai na kimanin mutane miliyan tun yayin da ta daura damarar ta'addanci tsawon shekaru goma da suka gabata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel