Majalisar Dattawa ta amince da sauya ranar Dimokuradiya a Najeriya

Majalisar Dattawa ta amince da sauya ranar Dimokuradiya a Najeriya

Majalisar Dattawan Najeriya ta yi shimfidar amanna kan kudirin amincewa da dokar ayyana ranar 12 ga watan Yuni a matsayin sabuwar ranar dimokuradiyyar kasar sabanin yadda ta kasance a baya na ranar 29 ga watan Mayu.

Shimfidar aminci na majalisar na zuwa ne bayan kimanin shekara guda da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi shelar cewa za a sauya ranar Dimokuradiya ta Najeriya daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni.

Majalisar Dattawa ta amince da sauya ranar Dimokuradiya a Najeriya

Majalisar Dattawa ta amince da sauya ranar Dimokuradiya a Najeriya
Source: UGC

A yayin da majalisar dattawan Najeriya yayin zaman ta na ranar Alhamis ta rattaba hannu kan wannan kudiri, majalisar wakilai ta tarayya a nata bangaren ta amince da wannan sabon kudiri tun a watan Dasumba na shekarar 2018 da ta gabata.

A yayin zaman ta bisa jagoranci mataimakin shugaban dattawa, Sanata Ike Ekweremadu, majalisar ta yi amanna da sabon kudirin yayin da shugaban ta mai rinjaye, Sanata Ahmed Lawan ya yi fashin baki na bukatar shugaban kasa Buhari.

KARANTA KUMA: Mayakan Boko Haram sun kashe Mutane 13 a Chadi

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari ya sauya ranar Dimokuradiyar kasar nan domin karrama Marigayi MKO Abiola a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 12 ga watan Yunin 1993.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel