NSGF ta kaddamar da wani muhimmin shirin farfado da tattalin arzikin arewa

NSGF ta kaddamar da wani muhimmin shirin farfado da tattalin arzikin arewa

Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa, NSGF ta kafa wata gidauniyar kudi a kan Naira biliyan shida domin farfado da tattalin arzikin yankin da kuma kawo cigaba.

Shugaban kungiyar mai barin gado, gwamna Kashim Shettima na jihar Borno ne ya bayar da wannan sanarwar yayin da ya ke bitan nasarorin da ya samu a shekaru hudu da suka gabata a ranar Juma'a a Kaduna.

Ya ce an dauki wannan matakin ne domin tabbatar da cewa yankin arewa ya fara dogoro da kansa a fanin samar da kudade.

Ya ce a karkashin shirin za a farfado da masakun yankin da kuma kamfanin New Nigeria Development Company (NDDC).

Gwamnonin Arewa sun kaddamar da shirin farfado da tattalin arzikin yankin

Gwamnonin Arewa sun kaddamar da shirin farfado da tattalin arzikin yankin
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Yanzu Yanzu: Kotu ta yanke hukunci kan sauya shekan Saraki da Dogara

Shettima ya ce ana sa ran gwamnonin jihohin arewa 19 ne za su tattaro kudin da za kamfanin za tayi amfani dashi. A halin yanzu sun tara Naira miliya 650.

"Domin cimma burin mu, ko wace jiha za ta rika bayar da gudunmuwar Naira miliyan 50 kowane wata na tsawon watanni shida.

"A halin yanzu, muna da N560 miliyan a cikin N5.7 biliyan da muke bukata. Ina kira ga jihohin da ba su cika alkawurransu ba da suyi kokarin yin hakan domin su samu damar fara ayyukan da muka tsara a karkashin shirin.

"Ayyukan sun hada da samar da kamfanin lantarki da zai iya samar da wuta mega watt 3000 zuwa 4000.

"Kungiyar kuma ta fara daukan matakan farfado da kamfanin New Nigeria Development Company, NDDC don ya cigaba da aikinsa a matsayin cibiyar kasuwanci da tattalin arziki na yankin arewa," inji shi.

Kungiyar kuma ta zabi gwamna Lalong na jihar Filato a matsayin sabon shugabanta da zai jagoranci kungiyar na shekaru hudu nan gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Online view pixel