An yankewa wani mutumi hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan an kama shi da laifin harbe saurayin 'yar shi

An yankewa wani mutumi hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan an kama shi da laifin harbe saurayin 'yar shi

- Kotu ta yankewa wani tsohon ma'aikacin NNPC hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan ta kama shi da laifin harbe saurayin 'yar sa

- Mutumin ya yi amfani da bindiga inda ya harbi saurayin har sau biyu, a take saurayin ya ce ga garinku nan

Wata kotun daukaka kara da take zaune a Calabar, jihar Cross River, ta amince da hukuncin kotun koli inda ta yankewa wani mutumi mai suna Godwin Elewana hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Elewana, tsohon ma'aikacin kamfanin man fetur na kasa (NNPC), ya roki kotun wacce ta yanke mishi hukuncin kisan bayan ta kama shi da laifin harbe wani matashi mai suna Douglas Ojugbo dan shekara 22 a duniya, wanda aka ce saurayin 'yar shi ne.

An yankewa wani mutumi hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan an kama shi da laifin harbe saurayin 'yar shi
An yankewa wani mutumi hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan an kama shi da laifin harbe saurayin 'yar shi
Source: Depositphotos

A lokacin da yake yanke hukunci akan mai laifin, alkalin kotun Justice Y. Ninpar ya ce:

"Kotun ta bincika dukkanin shaidun da ake da su akan mai laifin, kuma ta samu hukuncin da kotun ta yanke daidai da mai laifin, kuma laifin ya yi daidai da shari'a."

KU KARANTA: An kama malamin makaranta ya yiwa dalibai hudu 'yan kasa da shekaru 12

"Masu gabatar da kara suma sun gabatar da hujjojin su game da mutumin da ake zargin, inda suka bayyana cewa ya yi hakan ne da gangan. Saboda ya harbi saurayin har sau biyu da bindiga."

Bisa ga sashe na 319 na dokar kasa, ya nuna cewa duk wanda ya yi kisan kai, za ayi masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit

Online view pixel