Kare martabar kasa ya kasance shine a gabanku, Wamakko yayi kira ga yan sanda

Kare martabar kasa ya kasance shine a gabanku, Wamakko yayi kira ga yan sanda

-Sanata Wamakko ya shawarci sabbin jami'an yan sandan asalin jihar Sakkwato da suyi aiki domin kare martabar jiharsu da kasa baki daya

-Wamakko yayi wannan kiran ne yayinda tawagar jami'an su goma suka kai masa ziyarar ban girma a gidansa na Sakkwato

Sabbin jami’an yan sandan da suka kammala makarantar horar da yan sanda (wato Nigeria Police Academy, Wudil) a shekarar da ta wuce ne suka samu wannan jawabi daga bakin sanata Wamakko.

Yan sanda guda 10 yan asalin jihar Sakkwato sun kaiwa sanata Aliyu Wamakko ziyarar ban girma, inda yayi kira agaresu da su ba aikinsu muhimmanci musamman wajen kare martabar kasa.

Kare martabar kasa ya kasance shine a gabanku, Wamakko yayi kira ga yan sanda

Kare martabar kasa ya kasance shine a gabanku, Wamakko yayi kira ga yan sanda
Source: UGC

KU KARANTA:Sakacin likitoci ya kashe min Uwargida - Oshiomole

Sanatan ya kara cewa, “ Ku tabbata kun maida hankali wurin kare rayuka da dukiyoyin yan Najeriya, kana kada ku manta da gidajen da kuka fito da kuma jiharku.”

Wamakko ya basu tabbacin cewa kofarsa a bude take a duk lokacin da suke da bukatar shawara. Jagoran jami’an ASP Saddam Yahayya yace, sun ziyarci sanatan ne domin yi mashi godiya akan irin goyon bayan da ya dade yana basu wanda ya hada da nasiha kai har ma da dukiyarsa.

A wani labari mai kama da wannan, Oshiomole yace sakacin likitocine yayi sanadiyar mutuwar uwargidansa.

Yayi matukar takaicin faruwar wannan lamarin inda har yaso ya shigar da kungiyar likitoci kara kotu domin ya bibiyi hakkin matar tasa.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel