Kotu ta tsare wani dan shekara 51 kan laifin lalata yarinya yar shekara 13

Kotu ta tsare wani dan shekara 51 kan laifin lalata yarinya yar shekara 13

- Wata kotun majistare da ke Ikeja a jihar Lagas tayi umurnin tsare wani mutumi dan shekara 51, Ukapi Agwu a gidan kurkuku

- Ana zargin mutumin da lalata yarinya yar shekara 13 ta karfin tuwo

- Mai shari'an, Sule-Amzat ta umurci yan sanda da su tura takardar shari’an zuwa ga Daraktan hukunce-hukunce don jin shawararsa

Wata kotun majistare da ke Ikeja a jihar Lagas, a ranar Juma’a, 17 ga watan Mayu tayi umurnin tsare wani mutumi dan shekara 51, Ukapi Agwu, wanda ake zargi da lalata yarinya yar shekara 13 a gidan yari.

Mai shari’a Olufunke Sule-Amzat, wacce bata saurari rokon wanda ake kara ba, tayi umurnin cewa a garkame shi a gidan kurkuku na Kirikiri.

Sule-Amzat ta umurci yan sanda da su tura takardar shari’an zuwa ga Daraktan hukunce-hukunce don jin shawararsa.

Rashin imani: Dan shekara 51 ya haikewa yarinya yar shekara 13

Rashin imani: Dan shekara 51 ya haikewa yarinya yar shekara 13
Source: Depositphotos

Ta dage zaman shari’an zuwa ranar 17 ga watan Yuni.

Wanda ake kara, wanda ke zama a yankin Ikorodu, Lagas na fuskantar tuhumar fade.

KU KARANTA KUMA: Kannywood: Dalilin da ya sa nake auri-saki – Adam Zango

Da farko, dan sanda mai kara, ASP. Benson Emuerhi, ya fada ma kotu cewa maai laifin ya aikata laifin ne a ranar 30 ga watan Afrilu, da misalin karfe 10 na sae a gida mai lamba 15, Community Avenue St., Irawo, Ikorodu, Lagas.

Emuerhi yayi zargin cewa wanda ake kara yayi wa yarinyar fyade ta karfin tuwo.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel