Gwamnatin Kaduna ta amince da N54m don zuba sabbin ayyukan ci gaba a karamar hukumar Kaura

Gwamnatin Kaduna ta amince da N54m don zuba sabbin ayyukan ci gaba a karamar hukumar Kaura

- Gwamnatin jihar Kaduna ta amince da naira miliyan 54 domin gudanar da sabbin ayyuka daban-daban a karamar hukumar Kaura

- Ayyukan da za a gudanar sun hada ginei-ginen famfon tuka-tuka, kwalbati, da kuma gyare-gyaren hanyoyi a yankunan karkara

- Shugaban karamar hukumar ya kuma bukaci mutanen, musamman manoma da makiyaya, da su guje ma ayyukan da ka iya haddasa rashin zaman lafiya

Gwamnatin jihar Kaduna ta amince da naira miliyan 54 domin gudanar da sabbin ayyuka daban-daban a karamar hukumar Kaura, a cewar Bege Katuka, Shugaban yankin.

Katuka ya fada ma kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a ranar Juma’a, 17 ga watan Mayu a Kaura cewa ayyukan da za a gudanar sun hada ginei-ginen famfon tuka-tuka, kwalbati, da kuma gyare-gyaren hanyoyi a yankunan karkara.

Ya sake ba mutanen yankin tabbacin mamajircewa domin cika masu bukatunsu, inda ya bukaci da su mara masa baya da bashi hadin kai domin tabbatar da nasarar manufofi da shirye-shiryensu.

Gwamnatin Kaduna ta amince da N54m don zabu sabbin ayyukan ci gaba a karamar hukumar Kaura

Gwamnatin Kaduna ta amince da N54m don zabu sabbin ayyukan ci gaba a karamar hukumar Kaura
Source: Depositphotos

Shugaban karamar hukumar ya kuma bukaci mutanen, musamman manoma da makiyaya, da su guje ma ayyukan da ka iya haddasa rashin zaman lafiya, duba ga cewa lokacin noma yayi.

KU KARANTA KUMA: Kannywood: Dalilin da ya sa nake auri-saki – Adam Zango

Ya bayyana cewa hukumar za ta gudanar da taron gari nan bada jimawa ba inda masu ruwa da tsaki za su tattauna kan ci gaban da aka samu zuwa yanzu.

“Makasudin shirin shine jin ra’ayoyin jama’a. Yana da matukar muhimmanci sannin halin da suke ciki da ra’ayoyinsu. Wannan shine abunda muke son yi,” inji shi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel