Tsananin duka da barazanar kisa yasa wani dattijo neman kotu ta raba auren dake tsakaninsa da matarsa

Tsananin duka da barazanar kisa yasa wani dattijo neman kotu ta raba auren dake tsakaninsa da matarsa

Tsananin duka da kuma yawan barazanar kisa da matarsa take yi masa yasa wani tsoho garzayawa kotu domin ta kawo karshen auren da ke tsakaninsa da matarsa, wacce suka shafe sama shekaru 30 suna tare

Wani tsoho mai shekaru 82 a duniya mai suna Godwin Akinola ya garzaya wata kotu da take unguwar Agege cikin jihar Legas, inda ya ke rokarta akan ta raba auren dake tsakaninsa da matarsa mai suna Anthonia, inda ya bayyana yadda yake shan dan karen duka a wurinta, sannan kuma takan yi mishi barazanar duka a lokuta da dama.

Hakazalika Akinola ya kara rokar kotun akan data ba su tazara a lokacin da za a cigaba da sauraron shari'ar saboda 'yan uwansu su sasanta tsakanin su.

Tsananin duka da barazanar kisa yasa wani dattijo neman kotu ta raba auren dake tsakaninsa da matarsa

Tsananin duka da barazanar kisa yasa wani dattijo neman kotu ta raba auren dake tsakaninsa da matarsa
Source: Facebook

"A kowacce ranar Allah sai Anthonia ta yi min dukan tsiya, bayan duka kuma kullum sai ta yi mini barazanar cewa za ta kashe ni.

"Munyi aure ni da Anthonia kimanin shekaru 30 da suka gabata, kuma yanzu haka muna da yaro tsakanin ni da ita wanda yake da shekaru 35 a duniya, amma duk da wannan jimawar da muka yi da ita bai hanata cin zarafi na ba."

KU KARANTA: Hanyoyin da za abi domin kare kai daga cutar hawan jini

Akinola ya ce bayan ya gaji da wahalar da matar tashi ta ke bashi, sai ya nemi ya rabu da ita, sai 'yan uwansa dana matarsa suka fara rokar shi akan kada ya rabu da ita saboda sun riga duk sun tsufa, rabuwar ba ta da wata amfani.

A karshe dai alkalin kotun, Mai Shari'a Patricia Adeyanju ta bai wa ma'auratan shawara akan su je su shirya junansu.

Sannan alkalin ta daga sauraron karar har zuwa ranar 22 ga watan Agusta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel