Yanzu Yanzu: Kotu ta yanke hukunci kan sauya shekan Saraki da Dogara

Yanzu Yanzu: Kotu ta yanke hukunci kan sauya shekan Saraki da Dogara

Wata babban kotu da ke zamanta a Abuja da zartas da hukuncin cewa sauya sheka da 'yan majalisu 53 suka yi a majalisar tarayya zuwa wasu jam'iyyun ya sabawa doka kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

A yayin zartas da hukuncin a ranar Juma'a 17 ga watan Mayu, Mai shari'a Okon Abang ya ce 'yan majalisar ba su gabatar da gamsasun dalilai da zai basu damar ficewa daga jam'iyyunsu ba.

Hukuncin ya biyo bayan wata kara ne Legal Defence Assistance Project (LEDAP), ta shigar na kallubalantar sauya shekar da shugaban majalisar Dr Bukola Saraki da Kakakin majalisa, Yakubu Dogara Yakubu Dogara da wasu 'yan majalisa 51 suka yi.

Yanzu Yanzu: Kotu ta yanke hukunci kan sauya shekan Saraki da Dogara

Yanzu Yanzu: Kotu ta yanke hukunci kan sauya shekan Saraki da Dogara
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Kotu ta bayar da umarnin a kamo Hadiza Gabon cikin awanni 24

LEDAP ta bukaci kotu ta umurci 'yan majalisar suyi murabus daga kujerunsu sakamakon sauya shekar da suka yi kuma su mayar da albashi da allawus din da suka karba tun bayan ficewa daga jam'iyyun da suka ci zabe a karkashin ta.

Kungiyar tayi ikirarin cewa 'yan majalisar sun fice daga jam'iyyunsu ne saboda son rai ba domin rabuwan kawunna a jam'iyyunsu ba kamar yadda doka ta tanada.

Sai dai Alkalin ya ware batun sanata Godswill Akpabio inda ya ce bai saba doka ba saboda ba a gabatarwa kotun wata hujja da ke nuna ya sauya sheka ba zuwa jam'iyyar All Progresives Congress (APC) ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel