Gwamnonin arewa za suyi taro domin tattauna tsaro da almajiranci

Gwamnonin arewa za suyi taro domin tattauna tsaro da almajiranci

Gwamnonin arewa suna gudunar da taro a jihar Kaduna yanzu inda suke tattaunawa a kan matsalar garkuwa da mutane, fashi da makami da hare-haren 'yan bindiga a jihohin Kaduna, Katsina, Sokoto, Zamfara da sauran jihohin arewa maso gabas na kasar.

Baya ga shugaban kungiyoyin gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, sauran gwamnonin da suka hallarci wurin taron sun hada da gwaman Sokoto, Aminu Tambuwal, gwamnan Katsina, Aminu Masari, gwamnan Filato, Simon Lalong da mataimakin gwamnan Benue, Benson Abonu.

Gwamnonin arewa za suyi taro domin tattauna tsaro da almajiranci

Gwamnonin arewa za suyi taro domin tattauna tsaro da almajiranci
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Kotu ta bayar da umarnin a kamo Hadiza Gabon cikin awanni 24

A lokacin rubuta wannan rahoton, sauran gwamnonin jihohin na arewa suna hanyarsu na isowa wurin taron da ake yi a gidan Sir Kashim Ibrahim a Kaduna.

Ana sa ran za a tattauna batuttuwa da suka shafi matsalar rashin tsaro da harkar noma da batun almajirai da ba su zuwa makaranta da sauransu.

Wata majiya ta ce, "akwai yiwuwar kungiyar za ta zabi sabon shugaba duba da cewa wa'addin tsohon shugaban ya kare kuma zai tafi majalisar dattawa inda zai wakilic mazabarsa a matsayin sanata."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Online view pixel