Majalisar wakilai ta tsige kayyade shekaru wajen daukar aiki

Majalisar wakilai ta tsige kayyade shekaru wajen daukar aiki

Majalisar wakilai ta soke dokar kayyadde shekaru a yayin neman aiki a ma’aikatun gwamnatin tarayya da sauran hukumomi.

Hakan ya biyo bayan koke koke da 'yan Najeriya ke yi kan yadda wadansu ma’aikatun gwamnati ke sanya dokar kayyade shekaru wajen daukan ma'aikata aiki.

Yan majalisan sun gabatar da dokar ne karkashin jagorancin Sergius Ogun (APC, Edo) da Babajimi Benson (APC, Lagos).

Dokar wacce aka karanta a gaban majalisa karo na biyu a 2018, ta shiga feggi na uku bayan karbuwa da ta samu daga yan majalisa da kuma kakakin majalisar wakilai a lokuta da dama.

Majalisar wakilai ta tsige kayyade shekaru wajen daukar aiki

Majalisar wakilai ta tsige kayyade shekaru wajen daukar aiki
Source: Twitter

Majalisar tace ta gabatar da wannan doka ne domin tabbatar da cewar ba a hana ma wani dan Najeriya samun aiki saboda dalili na shekaru.

KU KARANTA KUMA: Zaben gwamnan Zamfara: Kotun koli za ta yanke hukunci kan APC a ranar 24 ga watan Mayu

Daya daga cikin yan majalisa da suka amince da dokar, Timothy Ngolu Simon, yace daya daga cikin dalilan da yasa Majalisa ta ce a cire wa'adin shekaru a mai’aikatun gwamnati da suke so su dauki ma'aikata aiki shine, akwai alamun ana bin son zuciya kuma ana karya doka wajen kin daukan 'ya'yan talakawa aiki.

Ngolu, shi kuma cewa ya yi akan kayyade shekaru a lokacin daukan 'yan sanda da sojoji wanda zai sa a zubar da matasa mararsa karfi da dama amma bai kamata ace an kayyade shekaru a dukkan Ma’aikatun gwamnati ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel