Zaben gwamnan Zamfara: Kotun koli za ta yanke hukunci kan APC a ranar 24 ga watan Mayu

Zaben gwamnan Zamfara: Kotun koli za ta yanke hukunci kan APC a ranar 24 ga watan Mayu

- An kammala komai don jin hukunci kotun koli kan zaben gwamnan Zamfara

- Majalisar mutum biyar karkashin jagorancin mukaddashin Shugaban alkalan Najeriya, Tanko Mohammed sun sanya ranar yanke hukunci

- Shugaban alkalan kasar ya sanar da ranar biyo bayan rokon cewa kotun ta duba hukuncin kafin ranar Laraba, 29 ga watan Mayu

Kotun koli a ranar Alhamis, 16 ga watan Mayu ta bayyana cewa za ta yanke hukunci akan karar da aka daukaka kan cire yan takarar jam’iyyar All Progressive Congress (APC) a jihar Zamfara a ranar Juma’a, 24 ga watan Mayu.

Kwamitin mutum biyar karkashin jagorancin mukaddashin Shugaban alkalan Najeriya, Tanko Mohammed sun sanya ranar yanke hukunci bayan sauraron korafe-korafe daga lauyoyin da ke ciki lamarin, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Mohammed ya sanar da ranar biyo bayan rokon cewa kotun ta duba hukuncin kafin ranar Laraba, 29 ga watan Mayu, domin kada a haddasa rikici a mulki a jihar.

Zaben gwamnan Zamfara: Kotun koli za ta yanke hukunci kan APC a ranar 24 ga watan Mayu

Zaben gwamnan Zamfara: Kotun koli za ta yanke hukunci kan APC a ranar 24 ga watan Mayu
Source: Depositphotos

Ranar 29 ga watan Mayu shine kundin tsarin mulki ta sani a matsayin ranar rantsar da sabbin gwamnoni a fadin kasar, illa ga jihohin da zabensu ya sha banbam.

Bangaren Gwamna Abdulazeez Yari na APC, wanda yayi nasarar lashe zaben fidda gwani na ranar 8 ga watan Oktoba , 2018 ta tunkari kotun kolin domin ta soke hukuncin kotun roko, reshen Sokoto.

KU KARANTA KUMA: Yan bautar kasa ma za su samu sabon albashi – Zainab Ahmed

Bangaren Sanata Kabiru Marafa ne ta shigar da rokon inda suke kalubalantar sakamakon zaben fidda gwanin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel