An kai farmaki sakatariyar APC, an sace takardu, na’urar sanyaya wuri, talbijin da sauransu

An kai farmaki sakatariyar APC, an sace takardu, na’urar sanyaya wuri, talbijin da sauransu

- Yan fashi sun fasa Sakateriayar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na jihar Ogun

- Sun sace takardu, na’urar sanyaya wuri, Talbijin da sauran abubuwan amfani

- Shugaban jam’iyyar, Derin Adebiyi ya bayyana cewa harin ya faru ne a yammacin ranar Laraba

Wasu wadanda ba a san su wanene ba sun kai farmaki sakateriyar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Ogun, inda suka tafi da kaya masu muhimmanci sannan suka lalata kaddarori.

Sun fasa rufin sama, sannan suka kwashi takardu, na’urar sanyaya wuri, injin jan ruwa, setin Talbijin da kujeru a ofisoshi da dama na sakateriyar.

Shugaban jam’iyyar, Derin Adebiyi, ya bayyana haka a ranar Alhamis yayin da yake gabatar da jawabai a taron manema labarai a Abeokuta.

An kai farmaki sakatariyar APC, an sace takardu, na’urar sanyaya wuri, talbijin da sauransu

An kai farmaki sakatariyar APC, an sace takardu, na’urar sanyaya wuri, talbijin da sauransu
Source: Facebook

Ya bayyana cewa harin ya faru ne a yammacin ranar Laraba, inda aka fasa ofisoshi hade da ofishin shugaban jam’iyyar na jihar, Sakateriya da na Sakatare mai shiryawa da sauran su.

KU KARANTA KUMA: Matsalar yiwa yara mata fyade na kara kamari a Kano – Yan sanda

Yayin da yake Allah wadai akan lamarin, Mista Adebiyi ya bayyana cewa ba a san manufar yan fashin ba amman akwai zatto, “tunda harin ya zo ne makonni biyu gabannin karewar gwamnatin Gwamna Amosun."

Har ila yau, yace an kai rahoton lamarin ga hukumomin tsaro don gudanar da bincike.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel