Matsalar yiwa yara mata fyade na kara kamari a Kano – Yan sanda

Matsalar yiwa yara mata fyade na kara kamari a Kano – Yan sanda

- Rundunar yan sandan jihar Kano tace lamarin yiwa yara mata fyade na kara hauhawa a jihar

- Hukumar tace ta samu kararrakin fyade 33 cikin makonni uku kacal

- Kakakin hukumar yace an tura wadanda ake tuhuma 25 kotu; yayinda har yanzu ake kan gudanar da bincike akan mutum takwas

Rundunar yan sandan jihar Kano tace lamarin yiwa yara mata fyade na kara hauhawa a jihar sakamakon samun kararrakin fyade 33 da hukumar ta samu cikin makonni uku kacal.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a jiya Alhamis, 16 ga watan Mayu, yace an tura wadanda ake tuhuma 25 kotu; yayinda har yanzu ake kan gudanar da bincike akan mutum takwas.

Matsalar yiwa yara mata fyade na kara kamari a Kano – Yan sanda

Matsalar yiwa yara mata fyade na kara kamari a Kano – Yan sanda
Source: UGC

Ya ambaci sanayen wadanda ake zargi a matsayin Imrana Abdullahi na Kabuga Qaurters, Kano; Isyaku Amadu na karamar hukumar Dawakin Tofa; Abubakar Hudu na kauyen Kachako karamar hukumar Takai; Bashir Sale na Sharada Quarters; Ilyasu Abubakar na Haye Quarters da kuma Ibrahim Isa na Yankaba Quarters, dukkaninsu a Nasarawa Quarters. Yace ana tuhumar wani Ibrahim Isa na Sauna Quarters kan laifi da ba haka kawai ba.

Yace dukkanin wadanda ake zargin sun amsa laifin cewa sun ci zarafin yaran da ake tuhumarsu a kai.

KU KARANTA KUMA: Garkuwa da mutane, fashi da makami: Gwamnonin arewa za su gana a Kaduna a yau

DSP Kiyawa ya kuma tabbatar da kamun wasu yan fashi da makami shida da suka addabi mazauna birnin jihar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel