Garkuwa da mutane, fashi da makami: Gwamnonin arewa za su gana a Kaduna a yau

Garkuwa da mutane, fashi da makami: Gwamnonin arewa za su gana a Kaduna a yau

- Gwamnonin arewa za su yi wata ganawa a yau Juma’a, 17 ga watan Mayu a jihar Kaduna domin tattauna matsalolin tsaro

- Za a yi ganawar ne a gidan gwamnatin Sir Kashim Ibrahim, Kaduna

- Za kuma su tattauna kundin tsarin sabon shugabancin kungiyar

Kungiyar gwamnonin arewa za su yi wata ganawa a yau Juma’a, 17 ga watan Mayu a jihar Kaduna domin tattauna matsalolin tsaro da ya addabi yankin arewacin kasar.

Hakan na kunshe ne a wani jawabi da Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima ya saki a jiya Alhamis, 16 ga watan Mayu.

A cewar sanarwar, za a yi ganawar ne a gidan gwamnatin Sir Kashim Ibrahim, Kaduna.

Garkuwa da mutane, fashi da makami: Gwamnonin arewa za su gana a Kaduna a yau

Garkuwa da mutane, fashi da makami: Gwamnonin arewa za su gana a Kaduna a yau
Source: Facebook

Ganawar zai tattauna akan ayyukan ta’addanci, fashi da makami, sace-sacen mutane da sauran matsalolin tsaro a yankin.

An tattaro cewa ganawar zai tattauna kundin tsarin sabon shugabancin kungiyar.

KU KARANTA KUMA: Ana wata ga wata: Gwamnan jihar Bauchi ya nemi a kafa dokar hana binciken sa bayan ya sauka daga mulki

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Kafatanin gwamnonin Najeriya sun bayyana amincewarsu da tsarin sakar ma kananan hukumomi da bangaren shari’a kudadensu kai tsaye ba tare da sun bi ta hannunsu ba, kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukata.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnonin sun bayyana haka ta kungiyar gwamnonin Najeriya ta bakin shugaban kungiyar, Gwamna Abdulaziz Yari na jahar Zamfara, a yayin taron kara ma juna sani akan aiwatar da tsarin da aka shirya a Otal din Transcorp dake Abuja a ranar Alhamis.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel