Mun amince da umarnin Buhari na sakar ma kananan hukumomi mara su yi fitsari – Gwamnoni

Mun amince da umarnin Buhari na sakar ma kananan hukumomi mara su yi fitsari – Gwamnoni

Kafatanin gwamnonin Najeriya sun bayyana amincewarsu da tsarin sakar ma kananan hukumomi da bangaren shari’a kudadensu kai tsaye ba tare da sun bi ta hannunsu ba, kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukata.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnonin sun bayyana haka ta kungiyar gwamnonin Najeriya ta bakin shugaban kungiyar, Gwamna Abdulaziz Yari na jahar Zamfara, a yayin taron kara ma juna sani akan aiwatar da tsarin da aka shirya a Otal din Transcorp dake Abuja a ranar Alhamis.

KU KARANTA: Shauki ya kama Buhari yayin daya kai ziyara zuwa kabarin Manzon Allah

A shekarar data gabata ne dai shugaba Buhari ya rattafa hannu akan dokar yantar da kananan hukumomi da bangaren shari’a a matakin jahohi ta hanyar mika musu kudadensu kai tsaya daga asusun gwamnatin tarayya.

Gwamna Yari wanda ya samu wakilcin gwamnan jahar Bauchi mai barin gado, Gwamna MA Abubakar ya bada tabbacin gwamnoni zasu yi aiki tare da Buhari don ganin sun aiwatar da wannan muhimmin tsari cikin ruwan sanyi.

“Na amince da bukatar shugaba Buhari na ganin bangaren sharia da kananan hukumomi sun samu yancin cin gashin kansu idan har ana bukatar Dimukradiyyarmu ta daure, hakan zai kara kaimi, sahihanci da kuma tsantseni a harkar gwamnati.” Inji shi.

Shima mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ike Ekweremadu a jawabinsa, ya jinjina ma wannan tsari, sai dai yace akwai bukatar a karfafa kananan hukumomi tare da yima dokokinsu garambawul.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Alkalan Alkalai na jahohi 34, Kaakakin majalisun dokokin jahohi 31, hadimin shugaban kasa akan harkar majalisa,Ita Enang, gwamnoni da sauran manyan baki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel