Manyan ayyuka 4 da nayi don janyo hankulan masu zuba jari zuwa Najeriya – Buhari

Manyan ayyuka 4 da nayi don janyo hankulan masu zuba jari zuwa Najeriya – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana manufarsa ta habakka hada hadar kasuwanci da zuba jari a Najeriya, wanda hakan zai samar da dimbin ayyuka ga matasa tare da kara karfin tattalin arzikin kasar gaba daya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Buhari wanda ya samu wakilcin gwamnan jahar Jigawa, Abubakar Badaru ya bayyana haka ne yayin taron hukumar kasuwanci ta kasa daya gudana a jahar Kaduna a ranar Alhamis, 16 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Shauki ya kama Buhari yayin daya kai ziyara zuwa kabarin Manzon Allah

A jawabinsa, shugaba Buhari yace ya gudanar da wasu muhimman ayyuka guda hudu wadanda ya tsarasu domin karkato da hankulan yan kasuwa masu zuba daga ciki da wajen kasar nan domin su zuba jari a Najeriya.

Buhari yace wadannan manyan ayyuka da gwamnatinsa tayi don janyo hankalin masu zuba jari Najeriya sun hada da farfado da sufurin jirgin kasa, gina sabbin hanyoyi, inganta wutar lantarki da kuma shawo kan matsalar tsaro a Najeriya.

“A lokacin da muka hau mulki a shekarar 2015, akwai kalubalen sufurin jirgin kasa, wutar lantarki da sauransu, haka zalika jahohi 24 zuwa 26 basa iya biyan albashi, amma cikin ikon Allah mun cigaba da aikin tituna 300 da muka tarar an yi watsi dasu, sa’annan mun bada aikin sabbin hanyoyi 100.

“A yanzu haka an kammala wasu, wasu kuma ana aikinsu, munyi haka ne domin rage cunkoson ababen hawa tare da saukaka sufurin mutane da kayansu, haka zalika mun gyara sufurin jirgin kasa domin jigilar kaya da mutane, haka nan muna kokari wajen gyaran wutar lantarki.” Inji shi.

Daga karshe shugaba Buhari ya bada tabbacin gwamnatinsa za tayi duk mai yiwuwa don ganin ta karkatar da akalar tattalin arzikin Najeriya daga man fetir zuwa wasu fannoni daban, musamman ma noma, don gudun kauce ma fadawa cikin tabarbarewar tattalin arziki irin na kasashen Venezuela da Angola.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel