Yan sandan Binuwe sun kama mutum 30 cikin mako guda

Yan sandan Binuwe sun kama mutum 30 cikin mako guda

-Yan sanda a jihar Binuwe sunyi nasarar cafke wasu mutum 5 yan kungiyar asiri a bisa aikata laifin fashi da makami

-A dadin dadawa mutanen na hannun yan sanda ana bincike kansu, daga nan kuma za'a zarce da su zuwa kotu inji DSP Anene

Rundunar yan sandan jihar Binuwe ta kama mutum 30 da laifuka daban daban a fadin Makurdi babban birnin jihar.

Jami’ar hulda da jama’a na rundunar, DSP Sewuese Anene wacce ta fayyacewa jaridar Daily Independent a Makurdi ranar Alhamis, tace daga cikin mutanen da aka kama mutum 5 yan kungiyar asiri ne.

Yan sandan Binuwe sun kama mutum 30 cikin mako guda

Yan sandan Binuwe sun kama mutum 30 cikin mako guda
Source: UGC

KU KARANTA:Nadin Emefiele: Wani dan majalisar APC ya mayar wa da Gudaji Kazaure martani

Tace an kama yan kungiyar asirin ne a daren Laraba yayinda suka kai samame a wata mashaya dake Makurdi.

A cewarta, "yan kungiyar sun iso mashayarne da misalin karfe 9 na dare inda suka fara sake albarushi a iska domin su firgita jama’a, hakan ne ya basu damar aikata fashi da makami a wannan mashaya".

"Bayan sun bar wurin ne muka samu nasarar damke 5 daga cikinsu, ko wannensu na dauke da zanen dake nuna alamar kungiyarsa a jikinsa.

Mun same su da kayayyaki kamar jakunkunan mata da sauransu. a halin yanzu dai muna bincike akansu sannan ba tareda jimawa ba zamu tura su kotu.

Mutane 14 daga cikin wadanda aka kama an rigaya da tura su zuwa kotu. Daga cikinsu kuma wadanda aka kama a bisa kuskure bayan mun fahimci cewa matafiyane duk an sake su, kamar yadda ta sanar da wakilin Daily Trust.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel