Dalilin da yasa muka dage gudanar da zaben gwamna a Kogi da Bayelsa – INEC

Dalilin da yasa muka dage gudanar da zaben gwamna a Kogi da Bayelsa – INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta bayyana dalilinta na dage gudanar da zabukan gwamnoni a jahohin Kogi da Bayelsa, kamar yadda ta sanar a ranar Alhamis, 16 ga watan Mayu.

Kaakakin shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, Rotimi Oyekanmi ne ya bayyana haka a daren Alhamis yayin daya bayyana a cikin wani shirin gidan talabijin na Channels, inda yace INEC ta dage zaben ne bayan samun korafi daga gwamnatin jahar Bayelsa.

KU KARANTA: Matasan Najeriya sun jinjina ma Buhari game da wani muhimmin aiki da yasa a gaba

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Onyekanmi yana fadin cewa mataimakin gwamnan jahar Bayelsa, John Jonah ne ya nemi hukumar INEC ta dage gudanar da zaben data shirya a ranar 4 ga watan Nuwamba duba da cewa ranar tayi daidai da ranar da ake bikin godiya ga Allah a Bayelsa, kuma dokar jahar ta amince da bikin.

“Idan zaku tuna a ranar 9 ga watan Afrilu ne muka saki jadawalin zaben gwamna a jahar Bayelsa da jahar Kogi da cewa zaben zai gudana ne a ranar 2 ga watan Nuwamba, sai dai gwamnatin jahar Bayelsa ta koka kan wannan rana ta hannun gwamnanta, kaakakin majalisar dokokin jahar, mataimakin gwamna, da kuma shuwagabannin addinai na cewa mu dage ranar.” Inji shi.

Sai dai Kaakakin har zuwa yanzu basu sanar da gwamnatin jahar Kogi batun dage zaben ba a hukumance, amma yace nan bada jimawa zasu sanar da jahar, tare da sanar da ita sabuwar ranar data sanya don gudanar da wannan muhimmin zabe.

Daga karshe Kaakakin yace yadda INEC ta gudanar da zabukan 2019 haka zata gudanar da zaben Kogi da Bayelsa, sai dai kawai yace zasu dauki darasi daga irin kura kurai da matsalolin da suka fuskanta a zabukan baya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel