Yadda yan Boko Haram suka tashi wasu garuruwan Adamawa cikin dare

Yadda yan Boko Haram suka tashi wasu garuruwan Adamawa cikin dare

Gungun mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram sun kaddamar da wani mummunan hari a wani kauyen dake cikin karamar hukumar Madagali ta jahar Adamawa, wanda hakan yayi sanadiyyar tserewar mazauna kauyukan don tsira da ransu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a daren Alhamis, 16 ga watan Mayu ne yan ta’addan suka diran ma kauyen Shuwa dake cikin karamar hukumar mulki ta Madagali, wanda bai wuce tazarar kilomita 7 zuwa karamar hukumar Michika ba.

KU KARANTA: Matasan Najeriya sun jinjina ma Buhari game da wani muhimmin aiki da yasa a gaba

Wani mazaunin kauyen daya tsere daga kauyen tun a cikin daren, Abuwa Kefas ya shaida ma majiyarmu cewa jama’a sun shiga halin rudani da tashin hankali sakamakon harin da mayakan Boko Haram suka kai musu babu zato babu tsammani.

“Wannan hari na cikin dare ya jefa jama’an karamar hukumar Michika cikin tashin hankali, wanda hakan ya sanya da dama daga cikinsu tattara inasu inasu suna tserewa tun a cikin daren domin tsira da ransu.” Inji shi.

Shima wani Sojan sa kai ya tabbatar da harin, inda yace a gabansa jama’an kauyukan Gulak da Duhu suna tserewa daga kauyukansu doin gudun kada mayakan na Boko Haram su karkata akalarsu zuwa kauyukan.

“Mayakan Boko Haram suna babbaka gidaje tare da shagunan mutane.” Inji shi. Sai dai duk kokarin da majiyarmu tayi na jin ta bakin kaakakin rundunar Sojan kasar Najeriya taci tura.

Sai dai har zuwa lokacin tattara wannna rahito babu tabbacin adadin mutanen da suka rasa ransu a sanadiyyar harin ko kuma suka jikkata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel