Babban bankin Najeriya na shirin farfado da masaku 50 cikin shekaru 4

Babban bankin Najeriya na shirin farfado da masaku 50 cikin shekaru 4

-CBN na shirin farfado da masaku guda 50 cikin shekaru hudu

-An kafa kwamitin da zai taimaka wurin farfado masana'antun masaka a Najeriya a karkashin babban bankin Najeriya CBN

Bayan dokar gwamanti ta haramta shigowa da auduga da sauran kayayyakin aikin masaka, babban bankin Najeriya wato CBN a jiya Alhamis ya kafa wani kwamiti domin farfado da masakun kasar nan.

Yayinda yake kaddamar da wannan kwamiti na sake farfado da masakun Najeriya a Abuja, gwamnan CBN Godwin Emefiele yace manufar kaddamar da wannan kwamiti dai shine a farfado da masaku 50 nan cikin shekaru 4 masu zuwa.

Babban bankin Najeriya na shirin farfado da masaku 50 a shekaru 4

Babban bankin Najeriya na shirin farfado da masaku 50 a shekaru 4
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Na hannun daman Atiku ya bukaci a bayyana sunayen masu shirin juyin mulki

“ Har yanzu Najeriya na cikin jerin kasashen dake kasuwancin masana’antar saka. Akwai bukatar mu karbe wannan masana’anta daga hannun yan fasa kwauri. Muna da bukatar taimakon kwastam da sauran hukumomin da abin ya shafa.” Emefiele ya fadi.

Yace kwamiti zai kasance ya maida hankali wurin sake farfado da masakun kasar nan wadanda aka mance dasu a baya. Bunkasa noman auduga na daga cikin ayyukan wannan kwamiti, ta yadda audugar zata wadaci ko ina fadin kasar nan.

Idan akayi nasarar yin wannan abu, sama da $2bn da muke asara ko wace shekara ta hanyar yan fasa kwauri dake shigowa da wadanda kayayyaki zai kau.

Ya kara da cewa, CBN zata hada hannu da hukumar kwastam domin dakatar da fasa kwauri, inda kuma anata zata samar da kyakkyawan yanayin gudanar da sana’ar ba tare da an tsawala haraji ba.

Wasu daga cikin gwamnonin da suka halarci kaddamar da wannan kwamiti sun hada da, Abdullahi Ganduje na Kano, mataimakin gwamnan Jigawa, Ibrahim Dankwambo na Gombe da kuma mataimakin gwamnan Kaduna Bala Barnabas.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel