Sakacin likitoci ya kashe min Uwargida - Oshiomole

Sakacin likitoci ya kashe min Uwargida - Oshiomole

-Shugaban jam'iyar APC yace skacin likitocine yayi sanadiyar mutuwar matarsa wai suna Ciara

-A lokacinda da abin ya faru nayi niyyar shigar da kungiyar likitoci kara kotu saboda sakacin sune ya kashe min matata, inji Oshiomole

Shugaban jam’iyar APC na kasa, Adams Oshiomole yayi kira akan a gyara tsarin aikin likitanci a kasar nan, ta yadda kowane likita zai yi aiki akan inda yafi kwarewa.

Oshiomole yace tangardar da ake samun a sashe likitoci wurin kulawa da lafiya abu wanda ke da saukin gyara idan har gwamnati ta maida hankali kai.

Kadan ya rage inyi karar likitoci a dalilin rasuwar matata, inji Oshiomole

Kadan ya rage inyi karar likitoci a dalilin rasuwar matata, inji Oshiomole
Source: UGC

KU KARANTA:Kotu ta bayar da umarnin a kamo Hadiza Gabon cikin awanni 24

Oshiomole wanda yayi jawabi wurin wani taro na musamman a asibitin koyarwa ta jami’ar Benin yace matarsa Ciara ta mutu a sanadiyar sakacin likitoci. Yace kadan ya rage ya kai likitoci kara kotu saboda sakacinsu ne yayi sanadiyar mutuwar matarsa.

“ Idan kaje asibiti zaka samu likita guda shine likitan mata, na kananan yara da kuma kwakwalwa duk shi dai. Abinda ya faru da matata a wancan lokacin shine an bata maganin wani abu daban yayinda ita kuwa ciwon daji ke damunta.

“ Wannan matsalar ta zama ruwan dare a asibitocinmu a yau. Gwamnati nada nata laifin a cikin wannan matsalar amma kuma muma muna da namu. Dalillin hakan ne yasa nake gina tawa asibitin wacce idan an kammalata zaku ga irin kayan aikin dake a cikinta.” A cewar Oshiomole.

A nashi jawabin wurin wannan taro, karamin ministan lafiya Dakta Ehanire Osagie ya yabawa asibitin UBTH na kaddamar da wannan gidauniya, inda yace bude gidauniyar zai ba asibitin damar tsayawa kafada da kafada da takwarorinta na sauran kasashen duniya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Online view pixel