Ana wata ga wata: Gwamnan jihar Bauchi ya nemi a kafa dokar hana binciken sa bayan ya sauka daga mulki

Ana wata ga wata: Gwamnan jihar Bauchi ya nemi a kafa dokar hana binciken sa bayan ya sauka daga mulki

- Kawunan yan majalisa ya rabu a majalisar dokokin jihar Bauchi biyo bayan wasu kudurori da gwamnan jihar mai barin gado ya nemi a gabatar

- Manufofi dai sun hada da samar da sabbin masarautu, da kuma soke wata kotu ta musamman da zata gudanar da bincike akansa idan ya sauka daga mulki

- Yan majalisa 17 cikin 30 sun nuna rashin amincewarsu

Kawunan yan majalisa ya rabu a majalisar dokokin jihar Bauchi biyo bayan wasu kudurori da gwamnan jihar mai barin gado, Muhammed Abubalar ya nemi majalisar ta amince dasu.

Wadannan manufofi dai sun hada da samar da sabbin masarautu, da kuma soke wata kotu ta musamman da zata gudanar da bincike akansa idan ya sauka daga mulki.

'Yan majalisa 17 daga cikin 30 sun ki amincewa da hakan a dalilin rashin bin kaidar ayyukan majalisar.

Wata sabuwa: Gwamnan jihar Bauchi ya nemi a kafa dokar hana binciken sa bayan ya sauka daga mulki

Wata sabuwa: Gwamnan jihar Bauchi ya nemi a kafa dokar hana binciken sa bayan ya sauka daga mulki
Source: UGC

Sai kuma dokar da 'yan majalisar ke son aiwatarwa shine wanda za a rika biyansu kudaden fansho na wata-wata a karshen zamansu a majalisa, ko da dai ba a gabatar da wannan batu ba a kwaryar majalisar.

KU KARANTA KUMA: Majalisar dattawa da fadar Shugaban kasa za su daina kwance wa juna zani a kasuwa idan na zama shugaba – Lawan Ahmed

Mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar, Abdullahi Abdulkadir shine ya karanta kudurorin da gwamnan ya aiko dasu domin su amince da su.

Sai dai a bangaren masu adawa da kudurorin sunce sam ba abi doka ba, kamar yadda dan majalisa dake wakiltar mazabar Lere Bula Muhammad Aminu Tukur yayi bayani ga manema labarai

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel