Nadin Emefiele: Wani dan majalisar APC ya mayar wa da Gudaji Kazaure martani

Nadin Emefiele: Wani dan majalisar APC ya mayar wa da Gudaji Kazaure martani

Kungiyar manyan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a majalisar wakilai sun caccaki Hon. Gudaji Kazaure (APC Jigawa) kan sake nadin gwamnan babban bankin Najeriya, Mista Godwin Emefiele.

A wani taron manema labarai a ranar Alhamis, 16 ga watan Mayu a Abuja, kakakin kungiyar, Hon. Abdulmumin Jibrin (APC Kano) ya bayyana cewa matsayar Kazaure akan lamarin bai yi daidai da matsayar kungiyar ba.

Kazaure ya bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya janye sake nadin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin kasar, cewa kungiyar magoya bayan Buhari, kungiyar kamfen din Buhari da kuma kungiyar yan kashenin Buhari basu ji dadin sake nadin nasa ba.

Ya kuma yi ikirarin cewa Emefiele bai yi kokari ba sosai a matsayinsa na gwamnan babban banki yayinda farashin naira ya tashi sosai akan farashin dala daga N180 zuwa N360 a karkashin kulawarsa.

Nadin Emefiele: Wani dan majalisar APC ya mayar wa da Gudaji Kazaure martani

Nadin Emefiele: Wani dan majalisar APC ya mayar wa da Gudaji Kazaure martani
Source: Facebook

Sai dai, Jibrin yace kungiyar masu ruwa da tsakin jam’iyyar a majalisar sun nesanta kansu daga matsayar Kazaure.

Kakakin kungiyar ya bayyana cewa masu ruwa da tsaki na APC na goyon bayan sake nada Emefiele.

Jibrin ya jaddada cewa Emefiele yayi namijin kokari akan kujerarsa.

KU KARANTA KUMA: Majalisar dattawa da fadar Shugaban kasa za su daina kwance wa juna zani a kasuwa idan na zama shugaba – Lawan Ahmed

Ya kara da cewa kungiyarsu nayi masa murna da fatan alkhairi, sannan sun bukaci da ya ci gaba da mayar da hankali ga aiki mai kyan da yake yi.

Jibrin yace Kazaure ya dauki wasa da nisa sosai sannan cewa kungiyar za su ci gaba da aiki da tattaunawa dashi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel