Majalisar dattawa da fadar Shugaban kasa za su daina kwance wa juna zani a kasuwa idan na zama shugaba – Lawan Ahmed

Majalisar dattawa da fadar Shugaban kasa za su daina kwance wa juna zani a kasuwa idan na zama shugaba – Lawan Ahmed

Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Ahmed Lawan, yace ya shiga tseren neman shugabancin majalisar ne domin kawo hadin kai a tsakani majalisun dokokin kasar biyu da kuma bangaren zartarwa.

Yace hakan na da matukar muhimmanci domin bangaren dokoki da na zartarwa za su yi aiki cikin aminci don Najeriya da kuma daukaka rayuwar al’umma kasar, inganta tattali arzikinsu, magance matsalolin tsaro saboda su samu dammar zama cikin lafiya da arziki.

Da yake jawabi ga manema labarai a jiya Laraba, Sanata Lawa, wanda ya kasance kan gaba wajen takarar shugabancin majalisa, yace hikimar jagoranci shine “hadin kai, hadin gwiwa da hada hannu” wadanda sune manyan manufofi wajen magance matsalolin kasa.

Majalisar dattawa da fadar Shugaban kasa za su daina kwance wa juna zani a kasuwa idan na zama shugaba – Lawan Ahmed

Majalisar dattawa da fadar Shugaban kasa za su daina kwance wa juna zani a kasuwa idan na zama shugaba – Lawan Ahmed
Source: Twitter

Yace babu fa’idar kwance ma juna zani a tsakanin bangaren dokoki da na zartarwa. “A inda ra’ayinmu ya banbanta, sai mu magance sabaninmu a cikin mutunci,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Wata yarinya ta kashe kanta bayan ta nemi abokanta na Instagram su taya ta zabi tsakanin mutuwa da rayuwa

Lawan yace Shugaban kasa Muhammadu Buhari na da tsare-tsare masu amfani sannan cewa zai bashi goyon baya wajen yiwa Najeriya da yan Najeriya aiki. Ya kuma ce zai yi aiki don kawo karshen rikicin gabatar da kasafin kudi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel