Mun kusa kammala bitar kasafin kudin 2019, inji ministar Kudi

Mun kusa kammala bitar kasafin kudin 2019, inji ministar Kudi

-Bitar kasafin kudin 2019 na zagaye na karshe, inji Zainab Ahmad

-Saura kiris mu kammala bitar kasafin kudin shekarar 2019, a cewar ministar kudi ta Najeriya

Zainab Ahmad ta sanar cewa bitar kasafin kudin shekarar 2019 ya kusa kammala yayinda da zarar hakan ya samu za’a kai shi zuwa ga shugaba Muhammadu Buhari.

Ta fadi hakan ne ranar Alhamis a Abuja yayin wata zantawa da manema labarai inda tayi magana akan yanayin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki a halin yanzu.

Munyi kusa kammala bitar kasafin kudin 2019, inji ministar Kudi

Munyi kusa kammala bitar kasafin kudin 2019, inji ministar Kudi
Source: UGC

KU KARANTA:FG ta samun kwato N605bn bayan kaddamar da dokar cinne domin tona asirin barayin gwamnati

Ministar tace an kai kasafin kudin gaban majalisar dokoki wanda tuni sun kammala duba shi inda suka dawo da shi fadar shugaban kasa domin a ya rattaba hannu.

A cewarta wannan bitar itace zata zamo ta karshe kuma ba zata dauki tsawon lokaci ba. Ta sake cewa dokar kasa ta bada damar tsara kasafin kudin ta yadda mafi yawancinsa zai kasance akan biyan albashi da kuma manyan ayyuka.

Wannan kasafin na 2019 yazo a daidai lokacinda na 2018 bai kare ba musamman lura da muhimman ayyukan cikinsa.

“ A yanzu haka muna da kasafi guda biyu wadanda doka ta bamu damar daukan kasha 50 cikin na shekarar data wuce domin ya taimaka mana wurin kaddamar da na bana.

“ Idan aka kammala bitar kana kuma aka kaddamar da kasafin 2019 zamu shigar da gaba daya abinda ya rage na daga kasafin 2018 saboda ya kasance bamu bar wani abu a tsakani ba.” Inji ministar kudi.

Ta sake tabbatar mana da cewa majalisar zartarwa a shirye take domin yin aiki da majalisar dokoki ta 9 ta yadda za’a dawo da tsarin Janairu zuwa Disemba wajen amfani da kasafin kudin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel