INEC ta daga zaben gwamna jihohin Bayelsa da Kogi

INEC ta daga zaben gwamna jihohin Bayelsa da Kogi

Hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC) ta sanar da cewar ta daga zaben gwamna a jihohin Bayelsa da Kogi daga ranar 2 ga watan Nwamba zuwa 16 ga watan Nuwamba na shekarar 2019.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban sashen ilimintar da masu zabe, Festus Okoye, INEC ta ce matsar da zaben ya zama dole ne bayan samun roko daga al'ummar jihar Bayelsa a kan bukatar hakan saboda ranar da hukumar ta tsayar tayi kacibus da ranar da jihar ke gudanar da bukukuwan addu'o'i na musamman, kamar yadda majalisar dokokin jihar tayi doka a shekarar 2012.

"Mun samu roko daga gwamnatin jihar Bayelsa, majalisar dokokin jihar, dattijai, shugabannin addini, sarakunan gargajiya, da ragowar masu ruwa da tsaki a jihar, a kan mu duba yiwuwar canja ranar zaben saboda tayi daidai da ranar da jihar ta ware a hukumance domin gudanar da addu'o'i na musamman.

INEC ta daga zaben gwamna jihohin Bayelsa da Kogi

Shugaban INEC; Mahmoud Yakubu
Source: UGC

"Bayn mun duba wannan bukata ta su, INEC, a zaman ta na mako mako da take yi duk ranar Alhamis, ta yanke shawarar matsar da ranar gudanar da zaben daga ranar Asabar 2 ga watan Nuwamba zuwa ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba na shekarar 2019," a cewar Okoye.

DUBA WANNAN: Abinda yasa ragowar kabilun Najeriya basu fahimci 'yan kabilar Igbo ba - Rochas

INEC ta kara da cewa ranakun gudanar da dukkan wasu al'amura da suka shafi zaben, zasu canja domin yin daidai da sabon kwanan watan da za a yi zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel