Mataimakin shugaban kasa ya jagoranci karashen zaman majalisar zantarwa

Mataimakin shugaban kasa ya jagoranci karashen zaman majalisar zantarwa

A halin yanzu cikin fadar shugaban kasa ta Villa da ke garin Abuja, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, na jagorantar karashen zaman majalisar zantarwa na wannan mako da yayi daidai da ranar Alhamis, 16 ga watan Mayun 2019.

Mataimakin shugaban kasa ya jagoranci karashen zaman majalisar zantarwa
Mataimakin shugaban kasa ya jagoranci karashen zaman majalisar zantarwa
Source: Facebook

Zaman majalisar na gudana ne sa'o'i kadan bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kama hanyar sa ta zuwa kasar Saudiya domin gudanar da Umara, a bisa amsa goron gayyata na masarautar Saudiya kamar yadda fadar shugaban kasa ta bayyana.

Majiyar jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, wannan shi ne karo na biyu da zaman majalisar ke gudana cikin wannan mako yayin da shugaban kasa Buhari ya jagoranci wanin sa a ranar Larabar da ta gabata.

KARANTA KUMA: Jihar Borno ta fi wasu jihohin Najeriya da dama kwanciyar hankali - Shettima

Jaridar mu ta Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari a ranar Laraba ya jagoranci zaman majalisar zantarwa da aka gudanar na tsawon awanni biyar, inda aka yanke shawarar gudanar da karashen sa a yau Alhamis domin tattauna wasu muhimman batutuwa da suka shafi kasar nan.

Rahotanni sun bayyana cewa, zaman majalisar zantarwa da mataimakin shugaban kasa ke jagorantar karashen sa ya fara gudana ne da misalin karfe 4.00 na Yammacin Alhamis cikin babban dakin taro na Council Chambers da ke garn Abuja.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel