FG ta samun kwato N605bn bayan kaddamar da dokar cinne domin tona asirin barayin gwamnati

FG ta samun kwato N605bn bayan kaddamar da dokar cinne domin tona asirin barayin gwamnati

-Tsarin tona asirin barayi da gwamnati ta kaddamar yana cigaba da samar da abinda ake so, a cewar Zainab Ahmad

-Kimanin N605bn ne tsarin ya samu damar bankadowa zuwa hannun gwamnati a yanzu

Gwamnatin tarayya ta fadi a ranar Alhamis cewa ta karbo N605bn bayan bullo da tsarin tona asirin barayin gwamnati wato ‘whistleblower policy.’

Ministar kudi, Zainab Ahmad itace da fadi adadin kudin ga manema labarai yayin wani taro na musamman a ofishinta dake Abuja.

FG ta karbo N605bn bayan kaddamar da dokar tona asirin barayin gwamnati

FG ta karbo N605bn bayan kaddamar da dokar tona asirin barayin gwamnati
Source: Twitter

KU KARANTA:Ana wata ga wata: PDP na tuhumar Buhari akan wasu makudan kudade

Tsarin tona asirin barayin wanda aka kaddamar a watan Disembar 2016, anyi shine domin kula da matsaloli cin hanci a cikin al’amuran gwamnati.

Taron dai ya samu halartar hukumomin dake karkashin ma’aikatar kudi ta kasa da kuma sauran masu ruwa da tsaki cikin aikin ma’aikatar.

Daga cikinsu akwai, shugaban hukumar fada da fasa kwauri ta kwastam Hameed Ali, shugaban DMO Patience Oniha, shugabannin Asset Management Corporation of Nigeria da kuma na Securities Exchange Commission.

Zainab ta bayyana tsarin tona asirin barayin da aka fito dashi a matsayin wata babbar nasara, inda ta kara da cewa N605bn da aka karbe an samu doriya ne akan abinda aka karba a baya.

Tace, “ Tsarin tona asirin barayi na nan yana cigaba da gudana kamar yadda ake so. Kuma adadin kudin da muka karbe tun bullo da tsarin sune N605bn. Wannan cigabane duba ga adadin da muka karbe a baya.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel