Dankari: Majalisar dokokin jihar Bauchi tayi dokar hana kwace kudin sata

Dankari: Majalisar dokokin jihar Bauchi tayi dokar hana kwace kudin sata

Majalisar dokokin jihar Bauchi ta zartar da dokar da ta warware dokar nan da ta bawa kotu damar bayar da izinin yin bincike tare da kwace kudade da kayayyaki da 'yan siyasa, ma'aikatan gwamnati da jama'a suka sata ko mayar wa mallakin su ta haramtacciyar hanya.

Kudirin da ya tsallake karatu na farko, na biyu da na uku a rana daya ba tare da fuskantar suka ba, na zuwa ne a yayin da ya rage saura sati biyu kacal wa'adin gwamnatin jihar ya kare bayan ta sha kasa a hannun jam'iyyar adawa a zaben da aka kammala.

Honarabul Abdullahi Abdulkadir, mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar, ne ya gabatar da kudirin, sannan ya samu goyon bayan Sale Nabayi, dan majalisa mai wakiltar mazabar Ganjuwa ta yamma, da Magaji Inuwa, dan majalisa mai wakiltar mazabar Jama'are.

Kawuwa Damina, shugaban majalisar dokokin jihar Bauchi, babu mamba ko daya, a cikin mambobi 13 da suka halarci zaman majalisar, da ya kalubalanci kudirin. Majalisar na da mambobi 31, amma 13 ne kawai suka halarci zamanta na ranar Alhamis.

Dankari: Majalisar dokokin jihar Bauchi tayi dokar hana kwace kudin sata

Majalisar dokokin jihar Bauchi
Source: Twitter

Ya ce zai tabbatar da cewar gwamnan jihar ya saka hannu a kan dokar, kuma an kaddamar da ita domin ta fara aiki nan take.

Honarabul Aminu Tukur, mamba mai wakiltar mazabun Lere/Bula, ya soki shugaban majalisar a kan amincewa da kudirin.

DUBA WANNAN: Ku daina cin shinkafar waje, akwai guba a cikin ta - Hameed Ali ya gargadi 'yan Najeriya

Ya kara da cewa akwai wata boyayyiyar manufa da ta saka shugaban majalisar zartar da dokar.

Kazalika, ya bayyana cewar mambobin majalisar da suka halarci zaman na hannun damar gwamnan jihar Bauchi, Mohammed Abubakar, ne, sannan ya kara da cewa sun yi zaman ne kafin lokacin da ya kamata majalisar ta zauna.

Idan gwamna Abubakar ya saka hannu a kan ta, dokar za ta warware wacce aka kirkira a shekarar 2017 domin taimaka wa gwamnati wajen karbo kudade da kayayyakin jama'a da masu mulki suka wawura ko mallaka wa kan su ta haramtacciyar hanya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel