Ku daina cin shinkafar waje, akwai guba a cikin ta - Hameed Ali ya gargadi 'yan Najeriya

Ku daina cin shinkafar waje, akwai guba a cikin ta - Hameed Ali ya gargadi 'yan Najeriya

Shugaban hukumar hana fasa kwabri ta kasa da aka fi kira da 'Kwastam', Kanal Hameed Ali (mai ritaya), ya roki 'yan Najeriya a kan su dain cin shinkafar da aka shigo da ita daga kasashen waje saboda akwai guba a cikin ta.

Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da yake gabatar da jawabi a wurin wani taro da ma'aikatar kudi ta shirya a Abuja.

Ali ya ce gwamnatin tarayya ba ta bayar da lasisin shigo da shinkafa ga kowa ba, a saboda haka duk shinkafar kasar waje da aka gani a Najeriya an shigo da ita ne ta barauniyar hanya.

Shugaban na Kwastam ya ce dukkan shinkafar da aka shigo da ita Najeriya na dauke da guba, saboda ta shafe a kalla shekara biyar a cikin rumbu.

"Akwai sinadari mai guba da ake zuba wa cikin shinkafar dake cikin rumbu don kar ta lalace.

Ku daina cin shinkafar waje, akwai guba a cikin ta - Hameed Ali ya gargadi 'yan Najeriya

Hameed Ali
Source: Depositphotos

"Sannan ana canja wa shinkafar buhu tare da canja kwanan wata don mu dauka sabuwa ce, hakan yasa muke kamuwa da cututtuka sakamakon cin irin wannan shinkafa.

DUBA WANNAN: Rundunar 'yan sanda tayi bajakolin masu garkuwa da mutane 93 da suka fitini hanyar Abuja

"Ina rokon 'yan Najeriya da su daina cin shinkafar kasar waje, mu ci tamu ta gida don mu zauna lafiya mu kuma taimaka wa hukumar kwastam wajen hana kasuwancin shinkafar waje," a cewar Ali.

Kazalika, ya bayyana cewar batun safarar shinkafar waje na daya daga cikin manyan kalubalen da jami'an kwastam ke fuskanta, ya kara da cewa ana cigaba da safarar shinkafar ne saboda har yanzu na amfani da ita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel