PDP ta nemi a sake a zaben gwamna a jihar Kwara

PDP ta nemi a sake a zaben gwamna a jihar Kwara

Dan takarar kujerar gwamnan jihar Kwara a karkashin inuwa ta jam'iyyar PDP, Razaq Atanwa, ya yi kira na neman kotun daukaka karar zabe akan bayar da umurnin sake gudanar da wani sabon zaben gwamna a jihar.

Kazalika jam'iyyar AA (Action Alliance) na ci gaba da kalubantar nasarar jam'iyyar APC ta zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Maris na 2019.

Dan takarar gwamnan Kwara na jam'iiyyar PDP; Razaq Atunwa

Dan takarar gwamnan Kwara na jam'iiyyar PDP; Razaq Atunwa
Source: UGC

Wannan kira na shigar da bukatar sake gudanar da sabon zaben gwamna a jihar Kwara, na zuwa ne yayin da a ranar Larabar da ta gabata aka fara sauraron karar korafe-korafen zabe kamar yadda majiyar mu ta bayar da shaida.

Kingsley Odeh, lauyan dan takara na jam'iyyar PDP, yayin shigar da korafin sa ya ce dan takara na jam'iyyar APC da ya lashe zaben gwamnan jihar, Alhaji Abdurrahman Abdulrazaq ba ya da cancantar tsayawa takara.

KARANTA KUMA: Gwamnati na ta yi tasiri wajen inganta rayuwar al'umma a jihar Legas - Ambode

Yayin gargadin lauyoyi akan kauracewa kawo tsaiko wajen gudanar da shari'a, Alkali Bassey Effiong ya nemi dukkanin masu korafi da su gabatar wa da kotu shaidu da kuma hujjoji na tuhumce-tuhumcen su.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel