Hukumar kiyaye hadura ta FRSC ta kama mutum 3000 bisa saba dokar tuki a birnin tarayya

Hukumar kiyaye hadura ta FRSC ta kama mutum 3000 bisa saba dokar tuki a birnin tarayya

-A cikin watanni 14 da suka gabata hukumar FRSC ta damke mutane 3000 a babban birnin tarayya da laifin amfani da wayar hannu

-Kakakin hukumar mai suna Mista Bisi Kazeem shine ya bayyanawa manema labarai wannan zancen a Abuja ranar Alhamis

Hukumar kiyaye hadura ta FRSC tace ta samu nasarar damke mutanen da yawansu bai gaza 3000 ba sakamakon amfani da wayar salula lokacin da suke tuki a babban birnin tarayya cikin watanni 14 da suka wuce.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Mista Bisi Kazeem shine ya bayyanawa kamfanin dillacin labarai na kasa wato NAN hakan ranar Alhamis a Abuja.

Hukumar kiyaye hadura ta FRSC ta kama mutum 3000 bisa saba dokar tuki a birnin tarayya

Hukumar kiyaye hadura ta FRSC ta kama mutum 3000 bisa saba dokar tuki a birnin tarayya
Source: Depositphotos

KU KARANTA:.Ana wata ga wata: PDP na tuhumar Buhari akan wasu makudan kudade

Kazeem ya bayyana laifin a matsayin abinda hukumarsu ko kokarin kawarwa saboda muninsa musamman akan manyan hanyoyi.

Yace “ Wannan mummunar dabi’a da direbobi key shekaru da dama zuwa yanzu yayi sanadiyar hadura da yawa. A sakamakon hadura kuma da yawa sun mutu inda kuma wasu suka samu nakasa ta har abada.

Domin haka, hukumarmu ta ayyana laifin a matsayin daya daga cikin manyan laifuka wanda take kokarin ganin bayansa a yanzu.

“ Wannan ne ya sanya hukumarmu ta fito da wani sabon tsari mai taken COBRA domin kula da direbobi wadanda aka same su da laifin yin waya a lokacinda suke tuki." Inji Mista Kazeem.

Kazeem ya bayyana mana cewa, daga watan Yulin 2017 zuwa watan Mayun 2019, sashen daga gudanar da sinitiri na hukumar FRSC ya samu kama mutane 4,914 wadanda aka aika dasu asibiti domin duba lafiyarsu.

Daga cikin mutanen da aka Kaman an samu wasu da rashin lafiyar kwakwalwa, wadanda yawansu ya kai 85.

Kakakin hukumar yace yana da yakinin nan bada jimawa ba yan Najeriya zasu fara kiyaye dokar rashin amfani da waya lokacin da suke tuki saboda yin hakan nada matukar muhimmanci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel