Na hannun daman Atiku ya bukaci a bayyana sunayen masu shirin juyin mulki

Na hannun daman Atiku ya bukaci a bayyana sunayen masu shirin juyin mulki

Dan gwagwarmaya kuma mataimakin sakataren yada labarai na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Kwamared Timi Frank ya kallubalanci Rundunar Sojin Najeriya ta gudanar da sahihin bincike ta kuma bayyana sunayen wadanda ke shirin kifar da gwamnatin Buhari idan hakan gaskiya ne.

A hirar da ya yi da manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, dan gwagwarmayar siyasan ya ce Rundunar Sojin tana shirya karerayi ne domin ta kare nasarar da shugaba Muhammadu Buhari ya samu kafin ranar 29 ga watan Mayu da za a rantsar da shi.

Frank ya yi ikirarin cewa, "ana shirya wata makirci na yiwa dan takarar shugabancin kasa na Jam'iyyar PDP sharri domin a kama shi ko kuma a kashe shi domin kare nasarar da aka sace daga hannunsa."

Zargin kifar da gwamnatin Buhari: An kallubalanci soji su fitar da sunayen wadanda ke shirya juyin mulki

Zargin kifar da gwamnatin Buhari: An kallubalanci soji su fitar da sunayen wadanda ke shirya juyin mulki
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Rikicin masarautar Kano: Bashir Tofa, Usman Bugaje da wasu manya sun saka baki

Ya ce kamata ya yi Buhari ya ki amincewa a rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu a matsayinsa na mutum kai gaskiya har sai kotun koli ta yanke hukunci kamar yadda shi (Buharin) ya yi a kan batun tsohon Alkalin Alkalai Walter Onnoghen."

A yayin da ya ke umurtan Lai Mohammed ya kyalle Atiku, Frank ya ce APC tana fargaba ne a yanzu inda ya ce ba a san Wazirin Adamawa ta tayar da fitina ba.

"Rundunar Soji da zama makamin farfaganda a karkashin gwamnatin Buhari amma kamar yadda na fadi a baya, idan har kotun koli bata sanar da wanda ya lashe zabe ba, gwamnatin APC za ta zama haramtaciya bayan ranar 29 ga watan Mayu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel