Matasan Najeriya sun jinjina ma Buhari game da wani muhimmin aiki da yasa a gaba

Matasan Najeriya sun jinjina ma Buhari game da wani muhimmin aiki da yasa a gaba

Matasan Najeriya sun yaba tare da jinjina ma gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa namijin kokari da kuma jajircewa da take yi wajen ganin ta habbaka noma a Najeriya, musamman noma shinkafa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito matasan sun bayyana wannan ra’ayi ne a yayin tattaunawa daban daban da suka yi da yan jaridu a jahar Gombe a ranar Alhamis 16 ga watan Mayu, kuma dukkaninsu masu sana’ar casar shinkafa ne.

KU KARANTA: Gwamna Ganduje ya kaddamar da manyan motocin sufuri guda 100 a Kano

Matasan sun tabbatar da cewa cigaba da aka samu a noman shinkafa a Najeriya ya samar da ayyukan yi ga dimbin matasan da a baya basu da aikin yi, sa’annan suna iya rike iyalansu da wannan sana’a a yanzu, tare da daukan wasu a karkashinsu.

Yusuf Adamu, guda daga cikinsu ya bayyana cewa shekara shida kenan yana aikin cashe shinkafa, kuma yace yana samun alheri matuka sakamakon tsare tsaren habbaka noma da Buhari ya kirkira, wanda hakan yasa suna samun aiki akai akai.

“A baya muna aiki ne kawai lokaci zuwa lokaci, amma sakamakon sauyin da Buhari ya kawo yasa muna samun aikin cashe shinkafa akai akai a yanzu, inda sayen shinkafa a Gombe da Adamawa, kuma ban taba rashinsa ba sakamakon akwaishi a kasuwanni yadda ya kamata.

“Hakan kuma ya tabbata ne sakamakon tallafin da gwamnatin Buhari ta baiwa manoma shinkafa ta hanyar basussuka da kayan aikin noma na zamani, don haka muma masu casar shinkafa muke amfana a kaikaice.” Inji shi.

Sai dai Adamu yace kalubalen da yake fuskanta duk da yana da matasa Arba’in dake aiki a karkashinsa shine matsalar wutar lantarki, saboda a cewarsa wutan da suke samu bai wuce awanni biyu ba a rana.

Shima wani mai suna Ibrahim Dorokudi ya bayyana cewa a rana suna cashe shinkafa buhu 160, kuma har su rage wasu sakamakon matsalar wuta duk kuwa da cewa suna biyan kudin wuta daya kai N30,000 a duk wata, amma basu samu abinda ya wuce sa’o’i biyu a rana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel