Mai dokar barci ya buge da gyangyadi: An kama jami’in tsaro da fashi da makami

Mai dokar barci ya buge da gyangyadi: An kama jami’in tsaro da fashi da makami

Rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Benuwe ta kama wani jami’in hukumar tsaron farin kaya, wanda ake kira da Civil Defence, NSCDC, tare da gurfanar dashi gaban kotu akan zargin aikata fashi da makami, wannan shine ana zaton wuta a makera sai aka tsinceta a masaka.

Legit.ng ta ruwaito rundunar ta gurfanar da jami’in tsaron mai suna Tersoo Chia dan shekara 36 ne gaban babbar kotun majistri dake garin Makurdi akan zarginsa da yi ma wani mutumi fashi da makami inda ya kwace masa N30,000 da kuma wayar hannu.

KU KARANTA: Rashin Imani ruwa ruwa: Yan bindiga sun yi garkuwa da jaririya yar wata 3 a Duniya

Dansanda mai shigar da kara, Sajan Friday Kansho ya bayyana ma kotu cewa daga ofishin Yansanda na Gboko aka maido da karar zuwa ofishin binciken manyan laifuka dake Makurdi a ranar 1 ga watan Afrilu, bayan wani mutumi mai suna Asemadoo Aor ya kai karar Chia zuwa ofishin Yansandan Gboko.

Aor ya bayyana ma Yansanda masu gudanar da bincike cewar a ranar 6 ga watan Feburairu ne jami’in tsaro Chia tare da wasu mutane biyu suka afka cikin gidansa dauke da bindigu da wukake inda suka yi masa fashin wayar hannu kirar Techo da kudi N30,000.

Shima Dansanda mai kara Kansho ya shaida ma kotu cewa a sakamakon binciken da suka kaddamar ne suka kama Chia, amma basu samu nasarar cafke sauran mutane biyun ba, suna cigaba da farautarsu.

Dansandan ya kara da cewa laifin da ake tuhumar Chia ya saba ma sashi na 6(b) dana 1(1)(2)(a)(b) na kundin dokokin yaki da fashi da makami da kuma daukan makamai ba bisa ka’ida ban a shekarar 2004.

Sai dai da lauyan wanda ake kara, Mista A. Amoomo ya nemi a bada belin wanda yake wakilta, inda yace Chia bashi da lafiya, yana fama da cutar hanta, don haka yana bukatar kyakkyawar kulawa, amma dansanda mai kara ya musanta bukatar bada belin.

Bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu ne sai Alkalin kotun, Isaac Ajim ya bada belin wanda ake kara akan kudi naira dubu 100, da kuma mutum guda da zai tsaya masa shima akan N100,000, sa’annan ya dage sauraron karar zuwa ranar 6 ga watan Yuni.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel