Tsohon jigo a APC ya soki bashin $1bn da Buhari zai karbo daga China

Tsohon jigo a APC ya soki bashin $1bn da Buhari zai karbo daga China

- Kwamared Timi Frank ya soki bashin dallar Amurka biliyan daya da gwamnatin tarayya za ta karbo daga China

- Tsohon jigon na APC ya ce gwamnatin tana ciwo bashin da za a bar jikokin mu da dawainiyar biya

- Dan siyasar dan asalin jihar Bayelsa ya yi kira ga 'yan Najeriya su tashi tsaye domin kare kansu daga sharin da gwamnatin APC ke janyowa a kasar

Tsohon mataimakin sakataren yada labarai na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Kwamared Timi Frank ya soki bashin dallan Amurka biliyan daya da gwamnatin tarayya ta karbo daga kasar China a kwana-kwanan nan.

A sanarwar da ya aike wa Legit.ng a ranar Alhamis 16 ga watan Mayu, Kwamared Franki ya ce gwamnatin tana ciwo bashin da zai jefa jikokin mu cikin fitina a Najeriya.

Tsohon jigo a APC ya soki bashin da Buhari zai karbo daga China
Tsohon jigo a APC ya soki bashin da Buhari zai karbo daga China
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Rikicin masarautar Kano: Bashir Tofa, Usman Bugaje da wasu manya sun saka baki

Ya kallubalanci gwamnatin ta yiwa jama'a bayanin abinda tayi da dallan Amurka biliyan daya da ta ciro daga asusun rarran man fetur kafin wannan.

Kalamansa: "Tambaya ta shine, mene ya ke yi da basusukan da ya rika karbowa tun lokacin da ya dare kan kujerar mulki? Ina kudaden da suka yi ikirarin sun kwato daga barayin gwamnati? Ina kuma kudaden da aka ce hukumomin gwamnati sun samar?

"Harkar tsaro na tabarbarewa. Rashawa ta munanan a karkashin Mai gaskiya. Fatara, rashin aikin yi da damfara suna abinda suka zama ruwan dare a karkashin gwamnatin APC."

Kwamared Frank ya yi kira ga 'yan Najeriya su tashi tsaye domin kare kansu daga sharin da gwamnatin APC ke janyowa a kasar.

Ya kuma yi kira ga kasashen duniya su ja kunnen sojojin Najeriya su dena jefa bakinsu cikin lamuran siyasar kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Online view pixel