Fasto ya nemi Gwamnatin Rotimi Akeredolu ta rika jin tausayin Talaka

Fasto ya nemi Gwamnatin Rotimi Akeredolu ta rika jin tausayin Talaka

Daily Trust ta rahoto cewa wani babban Fasto a Ondo, yayi kira ga gwamna mai-ci Oluwarotimi Akeredolu, da ya sauya rawar gwamnatin sa domin Talaka da maras gata su rika samun sauki a jihar.

Shugaban cocin nan na “Cherubim & Seraphim unification” da ke jihar Ondo watau Primate Ade Ademisokun Torton ya nemi mai girma Gwamna Rotimi Akeredolu, ya canza irin tsarin mulkinsa, ya kuma rika tauna kalaman sa.

Babban Faston yace irin maganganun da gwamnan yake yi da kuma akidunsa, za su sa Abokan hanayyarsa su samu galaba a kan sa a siyasance, wannan ya sa Malamin yayi kira da gwamnan na APC tun wuri, da ya sake nazari.

Malamin yake cewa abin farko da gwamnan ya soma yi a lokacin da ya karbi mulki shi ne kara kudin makaranta da kuma kudin ganin Likita a jihar Ondo. Wannan abu da gwamnan ya soma da shi, ya batawa mutanen jihar rai sosai.

KU KARANTA: Oshiomhole da wasu manyan APC sun hada Okorocha da EFCC

Fasto ya nemi Gwamnatin Rotimi Akeredolu ta rika jin tausayin Talaka

An gargadi Gwamnan Ondo ya canza salon mulki tun wuri
Source: Depositphotos

Haka zalika wannan Malami ya nunawa gwamnan cewa da ace ya san yadda aka yi samu tikitin takarar gwamna a APC, da tuni ya gyara salon mulkinsa domin a cewarsa, manyan APC da ke bada tutar jam’iyya, ba su tare da shi.

Wannan Fasto yake cewa a lokacin da ‘Yan APC su ka gaza takawa gwamnan burki ta hanyar kotu, sai su ka koma harinsa a jam’iyya, har ta kai aka dakatar da shi. Faston yayi kira ga gwamnan da ya dage wajen yi wa jama’a aiki.

Bayan nan kuma wannan Limami, ya bayyana cewa duk mukaman da ake badawa a Yankin Kudu su na karewa ne a hannun ‘Yan Legas, sannan kuma yace a daina yi wa ‘Yan majalisa shiga sharo ba shanu wajen zaben shugaban su.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel