Shugabancin majalisa baya bukatar garaje –Lawan

Shugabancin majalisa baya bukatar garaje –Lawan

-Sanata Lawan Ahmad yace zai gudanar da majalisa wacce yan kasa ke so idan ya kasance ya zamo shugaban majalisar dattawa

-Sanatan yayi wannan furucin a birnin tarayya yayinda yake zantawa da yan jarida

Dan takarar shugabancin majalisar dattawa sanata Lawan Ahmad yace ba zai kasance mai kawo cikas ba a harkokin majalisar dokoki idan aka zabe shi ya zama shugaban majalisar, saboda aikin bai son garaje.

Sanatan yace duk abinda zai amince ko kuma yaki amincewa dashi sai ya zama daidai da ra’ayin yan kasa.

Shugabancin majalisa baya bukatar garaje –Lawan

Shugabancin majalisa baya bukatar garaje –Lawan
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Yanzu-yanzu: Majalisa ta tabbatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban banki karo na biyu

Lawan wanda yake tare da shugaban yakin neman zabensa sanata Yahaya Abdullahi, yace a karkashin mulkinsa majalisar dokoki ba zata bata lokaci kafin kaddamar da kasafin kudi ba, inda yace cikin wata uku zasu gama da matsalarsa.

Da yake zantawa da manema labarai a birnin Abuja, sanata Lawan yace dalilin tsayawa takararsa domin shugabancin majalisar shine don ya taimaki majalisar zartarwa bisa alkawarin da sukayi wa yan Najeriya a lokacin zabe.

Lawan ya sake cewa, “ Kudurinmu a matsayinmu na majalisar dokokin ta kasa,shine muyi aiki domin yan Najeriya saboda mun san cewa sunada bukatar gwamnati wacce zata iya daukar nauyinsu a bangarori da dama.

“ Dole mu hada kanmu waje daya, sannan maganar bambancin jam’iya ma mu manta da ita. Hakan shine zai bamu damar yin aiki a tare domin kawowa kasarmu cigaba.” Inji sanata Lawan.

Ya sake jaddada kudurinsa na gudanar da majalisa wacce yan Najeriya zasu ga amfaninta yana nan har ili yau.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel