Nadin sarakuna: Kwamishinan Ganduje yayi karin haske kan umarnin Kotu

Nadin sarakuna: Kwamishinan Ganduje yayi karin haske kan umarnin Kotu

- Barista Ibrahim Mukhtar ya karyata cewar an dakatar da kafa sabbin masarautu a Kano

- Atoni-janar na jihar Kano yace maimakon haka kotu kawai Kotu tace ka da wanda ya kawo wani sabon tsari

- Mukhtar yace lamarin ya rigada ya wakana kafin a bayar da umurnin

Atoni-janar na jihar Kano, Barista Ibrahim Mukhtar ya karyata rahotannin cewa an dakatar da kafa sabbin masarautu a Kano.

Yayin da yake mayar da martani akan lamarin, Mukhtar ya musanta ikirarin tare da bayyana cewa kotun tace ta daga sauraran karan zuwa ranar 21 ga watan Yuli, sannan ta nemi a bar masarautun yadda su ke.

Ya ce kundin tsarin mulkin kasar bata amince da karya dokar kotu.

Nadin sarakuna: Kwamishinan Ganduje yayi karin haske kan umarnin Kotu

Nadin sarakuna: Kwamishinan Ganduje yayi karin haske kan umarnin Kotu
Source: Facebook

Alkalan-alkalan har ila yau ya bayyana cewa lamarin gwamnatin jihar Kano dangane da rashin bin umurnin kotu kan kafa sabbin masarautu, ya kasance saboda umurnin ya biyo bayan afkuwar lamarin da ake kalubalanta ne.

Ya kara da cewa an kammala nadin sarakunan da mika sandunan girma gare su kafin a gabatar masu da umurnin kotun.

KU KARANTA KUMA: Yan Hisbah sun kama mutum 80 kan laifin cin abinci a bainar jama’a a lokacin Ramadan

Wani dan majalisan, mai wakiltan mazabar Gwarzo Rabiu Sale Gwarzo ne ya shigar da karan yana kalubalantan kafa sabbin nasarautun.

Wadanda ake tuhuma sun hada da ofishin gwamnan jihar, kakakin majalisan dokokin jihar Kano, akawun majalisan da kwamishinan sharia.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel