Ademola Adeleke ya kuma burmawa cikin wata sabuwar shari’a da ‘Yan PDP

Ademola Adeleke ya kuma burmawa cikin wata sabuwar shari’a da ‘Yan PDP

‘Dan takarar jam’iyyar hamayya ta PDP a zaben gwamnan jihar Osun da aka yi a shekarar bara, Sanata Ademola Adeleke, ya sake samun kan sa a gaban Alkali a cikin wata danyar shari’a da 'yan cikin-gida.

Kamar yadda mu ka samu labari a makon nan, wasu ‘Ya ‘yan jam’iyyar PDP sun shigar da ‘dan takarar na su a zaben Osun gaban kotu ne da nufin ayi bincike a game da takardun shaidar karatun Boko da ya gabatarwa hukumar INEC.

Wasu ‘Ya ‘yan PDP a karkashin wata tafiya ta “Concerned PDP Members”, sun nemi Alkalin babban kotun tarayya da ke zama a babban birnin Osogbo na jihar Osun, da ya binciki duk satifiket din ‘dan takarar gwamnan na 2019.

Wani Bawan Allah mai suna Ajayi Shuaib, shi ne ya shigar da kara a madadin kungiyar “Concerned PDP Members”, inda yake nuna shakku a kan sahihancin takardun kammala sakandaren da Ademola Adeleke ya mikawa INEC.

KU KARANTA: Kotu ta ba APC gaskiya bayan Gwamna Oyetola ya daukaka kara

Ademola Adeleke ya kuma burmawa cikin wata sabuwar shari’a da ‘Yan PDP
Sanata Adeleke yana ganin ta kansa bayan an sake maka sa a Kotu
Asali: Depositphotos

Daga cikin wadanda ake kara a shari’ar akwai uwar jam’iyyar PDP mai adawa da ta tsaida Sanata Ademola Adeleke a matsayin ‘dan takararta, da kuma hukumar INEC da ta tantance sa bayan ta duba duk takardun da ya gabatar.

Ajayi Shuaib ta bakin Lauyansa watau Barista Seyi Oyagbile yana ikirarin cewa takardun da ‘dan takarar jam’iyyar na su ya mika ba su inganta ba. Lauyan ya nemi kotu tayi wa wani sashe na doka ta 182(1) na tsarin mulki fashin baki.

Seyi Oyagbile yana so kotu ta duba ta gani ko takardun ‘dan takarar sun inganta da har zai tsaya takara, ko kuma takardun jabu ne ya gabatar don haka ayi watsi da takarar gwamnan da yayi a karshen 2018.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel