Gayyatar Buhari ya je ya yi Umarah daraja ce aka baiwa Najeriya – Fadar Shugaban kasa

Gayyatar Buhari ya je ya yi Umarah daraja ce aka baiwa Najeriya – Fadar Shugaban kasa

Kakakin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ya bayyana tafiyar Umarah da Shugaban kasar yayi a matsayin daukaka kasar Najeriya a idon duniya.

Yace: ''a idon duniya gayyatar Shugaba Buhari ya je ya yi Umarah, daraja ce da kima aka baiwa kasar.''

Garba yayi Karin haske akan yamutsa gashin baki da wasu yan Najeriya ke yi kan yawan tafiye-tafiye da Shugaban kasar je yi zuwa kasashen ketare, inda yace ba za a taba rasa hassada a zukatan masu irin wannan korafi ba, sannan kuma ya bayyana cewa babu adalci a cewar wai Buhari ba ya cika zaman kasar.

A yau Alhamis, 16 ga watan Mayu ne dai jirgin Shugaban kasar ya lula zuwa kasa mai tsarki domin yin aikin Umarah.

Gayyatar Buhari ya je ya yi Umarah daraja ce aka baiwa Najeriya – Fadar Shugaban kasa

Gayyatar Buhari ya je ya yi Umarah daraja ce aka baiwa Najeriya – Fadar Shugaban kasa
Source: UGC

Hakan ya biyo bayan gayyatar da sarkin Saudiyya, Salman Bin Abdulaziz yayi masa domin yin aikin Umarah a cikin wannan wata mai tsarki na Ramadan.

Ana sa ran zai koma gida Najeriya ranar Talata 21 ga watan Mayu.

KU KARANTA KUMA: Yan Hisbah sun kama mutum 80 kan laifin cin abinci a bainar jama’a a lokacin Ramadan

Ziyarar ta wannan karon na zuwa ne mako biyu bayan mahukuntan kasar sun sako Zainab Aliyu wata daliba 'yar Najeriya da suka zarga da safarar miyagun kwayoyi bayan shafe wata hudu a tsare.

Musulmi da dama kan yi Umara cikin watan Ramadan saboda falalar da watan ke da ita.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel