Yanzu-yanzu: Majalisa ta tabbatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban banki karo na biyu

Yanzu-yanzu: Majalisa ta tabbatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban banki karo na biyu

- Yanzun nan majalisar zartaswa ta Najeriya ta tabbatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) a karo na biyu

- Gwamnan wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikawa majalisar makon da ya gabata akan ta tabbatar da shi, ya samu karbuwa a yau

A yau Alhamis dinnan ne majalisar dattijai ta tabbatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnnan babban bankin Najeriya (CBN) a karo na biyu, inda zai kara shafe wasu shekaru biyar a bankin.

Tabbatarwar ta biyo bayan rahhoton da majalisar dattijai ta fitar akan banki, da sauran cibiyoyin harkokin kudi, wanda Sanata Rafiu Ibrahim (PDP Kwara) ya jagoranta.

A makon da ya gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dokoki akan sanya hannu domin tabbatar da gwamnan babban bankin a karo na biyu.

Yanzu-yanzu: Majalisa ta tabbatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban banki karo na biyu

Yanzu-yanzu: Majalisa ta tabbatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban banki karo na biyu
Source: Depositphotos

Sakamakon haka, a ranar Talatar nan da ta gabata majalisar ta ware wani kwamiti karkashin shugabancin Sanata Rafiu Ibrahim, inda suka tantance shi kuma suka bayar da rahoton sakamakon.

Kwamitin ta gana da Emefiele a jiya Laraba inda dukkan mambobin kwamitin suka yi na'am da komawar tashi a karo na biyu.

KU KARANTA: Obasanjo ne mutumin da yafi kowa cin amana a Najeriya - Sarkin Legas

Da yake gabatar da rahoton yau Alhamis, Ibrahim ya ce kwamitin ta kammala bincike kuma ta samo sakamako kamar haka: "Kwamitin ta samu cewar Emefiele ya yi aiki sosai a lokacin da ya gabatar da aikinsa karo na farko, kuma yana da kwarewar da ake bukata don ya cigaba da jagorantar bankin a karo na biyu."

Bayan ya kammala gabatar da sakamakon, majalisar ta yanke shawarar tabbatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin a karo na biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel