Zargin karkatar da kudade: EFCC ta titsiye Akawun majalisar tarayya na tsawon awanni

Zargin karkatar da kudade: EFCC ta titsiye Akawun majalisar tarayya na tsawon awanni

Hukumar yaki da rashawa, EFCC ta gayyaci magatakardan majalisar tarayya, Mohammed Sani-Omolori domin amsa tambayoyi game da wasu kashe-kashen kudade da aka gudanar a majalisar.

Sahara Reporters ta kuma ruwaito cewa baya ga tambayoyi game da yadda ake kashe kudaden majalisar, an yiwa Sani-Omolari tambayoyi a kan yadda ake gudanar da zaben shugabanin majalisar karo na 9.

Jami'an na EFCC sun masa tambayoyi na tsawon sa'o'i shida daga karfe 11 na safe zuwa 5 na yamma.

Zargin karkatar da kudade: EFCC ta titsiye Akawun majalisar tarayya

Zargin karkatar da kudade: EFCC ta titsiye Akawun majalisar tarayya
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Rikicin masarautar Kano: Bashir Tofa, Usman Bugaje da wasu manya sun saka baki

Hukumar na yaki da rashawa da masu yiwa arzikin kasa ta'annati ta tambayi magatakardan majalisar tsarin da aka bi wurin zaben wasu masu rike da manyan mukamai na majalisar karo na 9.

Sani-Omolari wadda EFCC ta kwacewa fasfo din tafiya kasashen waje ya bawa jami'an hadin kamar yadda rahotanni suka bayyana.

An gano cewa hukumar ta EFCC ba za ta kyalle duk wani mai rike muhimmin mukami da majalisar ba a binciken ta.

An gano cewar za ta gayyato magatakardan Majalisar Dattawa, magatakardan Majalisar wakilai na tarayya da mataimakansu domin amsa tambayoyi a nan gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel